Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai ba gwamna shawara kan jam’iyyun siyasa a jihar Katsina hon Shu’aibu Duwan ya faɗi haka a wata hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce sabuwar jam’iyar ADC har yanzu bata zauna da ƙafafuwan ta ba, “Mutane na ɗari ɗari da su saboda sun san ko su waye ke cikin ta shi yasa babu wanda ya kusance ta,”Inji Duwan.
A cewar sa ita kuwa jam’iyar adawa ta PDP babu ita ma sam sam daga sama har ƙasa”a nan Katsina mutum ɗaya ke kiɗan sa yake rawar da,”Inni ji mai ba gwamna shawara.
Ya ce gwamnatin APC ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa a kullum zuba ayyuka na alheri ta ke yi a faɗin jihar.
“Dikko ya gina manyan da gyara manyan asibiti baya ga ɗaukaka wasu ƙananan asbitoci zuwa manya a shiyar Katsina, Funtua da Daura,”inji Duwan.
Haka kuma mai ba gwamna shawara kan jam’iyu ya cigaba da bayyana wasu abubuwan more rayuwa da gwamnan ya samar da suka haɗa da gina manyan hanyoyi da gyaran wasu a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa Dikko Raɗɗa ya gina sabbin makarantu na firamare da sakandare tare da ɗaukan malaman makaranta fiye da dubu bakwai da kuma samar da isasshen takin zamani da sauran kayan noma.
Duwan ya bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatin ta yi kan tsaro da ya ce ana samun nasara da sauran aikace aikace na bunƙasa jihar da Dikko ya aiwatar.
Yace duka waɗannan nasarori da gwamna Raɗɗa ya samu a ƙarƙashin jam’iyar APC ce wanda yasa kowa ya gamsu da jagorancin jihar.
Domin haka yayi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da bai wa gwamnatin Dikko Raɗɗa goyon baya ta cigaba da aiwatar da ayyuka na alheri a jihar.
