Bankin Duniya ya buƙaci Nijeriya ta inganta tallafi bayan raba biliyan N658.9 ga talakawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta raba jimillar Naira biliyan 658.9 a matsayin tallafin kuɗi kai tsaye ga gidaje miliyan 10.46 na talakawa da masu rauni a Nijeriya zuwa watan Satumban 2026. Sai dai Bankin Duniya ya buƙaci gwamnati ta faɗaɗa shirin, ƙara adadin tallafin da ake bayarwa tare da tabbatar da cewa masu cin gajiyar shirin na samun kuɗaɗen a kai a kai.

Bankin ya ce, ya kamata gwamnati ta gina bisa nasarorin da aka samu wajen samar da ingantaccen tsarin tallafa wa al’umma na dogon lokaci, maimakon dogaro da matakan agajin gaggawa kawai wajen rage wa ’yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi raɗaɗin matsin tattalin arziki.

Wannan shawara na ƙunshe ne cikin sabon rahoton Bankin Duniya kan ci gaban Nijeriya mai taken, “Bayan Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya: Yadda ƙarin Kuɗaɗen Shiga Ya Shafi Abubuwan da Jihohi Suka Ba Fifiko”. An yi nazarin rahoton ne ranar Lahadi, inda aka duba halin tattalin arzikin ƙasar da kuma rawar da matakan gwamnati ke takawa wajen rage wa iyalai wahalhalun kuɗi. A cewar rahoton, Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da na’urorin tantance halittar jiki da tsarin zamani na dijital wajen gano waɗanda suka cancanci tallafin da kuma tabbatar da isar da kuɗaɗen gare su.

Bankin Duniya ya bayyana cewa ingantaccen tsarin tallafa wa al’umma da samar da hidimomin gwamnati yadda ya kamata na taimakawa wajen kare iyalai daga illolin matsin tattalin arziki. Sai dai ya yi gargaɗin cewa tasirin irin waɗannan shirye-shirye ya danganta da yawan mutanen da suka amfana, wadatar tallafin da ake bayarwa da kuma yadda ake biyan kuɗaɗen a kai a kai.

Rahoton ya ce, “Tallafa wa al’umma da ingantaccen samar da hidimomi na iya rage wa iyalai raɗaɗin waɗannan matsaloli, amma tasirinsu zai ci gaba da dogaro da yawan waɗanda suka amfana, wadatar tallafin da kuma ci gaba da biyan kuɗaɗen ba tare da yankewa ba.”

Bankin ya lura cewa, duk da cewa tallafin naira biliyan 658.9 ya isa ga miliyoyin gidaje masu rauni, akwai buƙatar faɗaɗa shirin da ƙarfafa yadda ake gudanar da shi domin ƙara inganta walwalar iyalan da suka amfana. A cewar bankin, Gwamnatin Tarayya ta bayar da rahoton raba naira biliyan 658.9 zuwa watan Satumban 2026 ga gidaje miliyan 10.46 na talakawa da masu rauni, ta hanyar amfani da na’urorin tantance halittar jiki da tsarin fasahar zamani wajen tantance masu cin gajiyar shirin da kuma isar musu da kuɗaɗen.

Rahoton ya buƙaci a hanzarta aiwatar da shirin tare da inganta yawan waɗanda ke amfana, adadin kuɗaɗen da ake ba su da kuma daidaiton lokacin biyan tallafin, domin ya samar da gagarumin sauki ga mutanen da ke fama da matsin tattalin arziƙi.

Ya ƙara da cewa, “Ya kamata a hanzarta kuma a zurfafa waɗannan ƙoƙarin, tare da ci gaba da faɗaɗa yawan masu cin gajiyar tallafin, inganta adadin kuɗaɗen da ake bayarwa da kuma tabbatar da daidaiton biyan su, domin ƙara faɗaɗa tasirinsu wajen inganta walwalar iyalai.”

Haka kuma, Bankin Duniya ya buƙaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su samar da tsarin samun kuɗaɗen gudanar da shirin na dogon lokaci. Ya ce samun tabbataccen tsarin kuɗaɗen gudanarwa zai zama wajibi domin tabbatar da ɗorewar tallafin da ake bai wa talakawa da sauran masu rauni.

Rahoton ya ce mataki na gaba bayan nasarorin da aka samu shi ne sauya tsarin daga agajin gaggawa zuwa ingantaccen shirin tallafa wa al’umma mai ɗorewa, wanda zai ƙunshi ware kasafin kuɗi na musamman a matakin tarayya da jihohi, ƙara yawan kuɗaɗen da gwamnatoci ke warewa a hankali da kuma samar da manufa guda da za ta haɗa dukkan ɓangarorin.

Wannan shawara ta kuma jaddada cewa gwamnatocin jihohi na da alhakin ƙara nasu gudummawar kuɗi wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi, maimakon barin mafi yawan nauyin gudanar da shirin a wuyan Gwamnatin Tarayya. Bankin ya bayyana cewa ware takamaiman kuɗaɗen tallafi a kasafin kuɗin tarayya da na jihohi zai taimaka wajen tabbatar da biyan tallafin a kan kari, tare da rage dogaro da shirye-shiryen wucin gadi. Haka kuma, samar da tsari guda na ƙasa zai inganta yadda ake gudanar da tallafin da kuma sa ido kan yadda ake rarraba shi.

A ƙarshe, Bankin Duniya ya yi kira da a koma ga tsarin tallafa wa al’umma mai tabbas da ɗorewa, wanda kuɗaɗen gwamnati za su ɗauki nauyinsa, tare da haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya masu rauni na samun tallafin da za su iya dogaro da shi.

By ukarofi

Leave a Reply