‘Yan sanda sun fara farautar maharan da suka kai wa Jarumi Tiger Shroff hari da bindiga

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Fitaccen jarumin fina-finan Bollywood, Tiger Shroff, ya tsallake rijiya da baya bayan wasu mahara sun buɗe wa motarsa wuta a birnin Mumbai na ƙasar Indiya, lamarin da ya jikkata wasu mutane biyu tare da jefa jami’an tsaro cikin gagarumin bincike domin gano waɗanda suka aikata harin.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026, a kusa da Pushpa Narsee Park da ke yankin Juhu, lokacin da jarumin ke shirin barin wurin bayan buga ƙwallon ƙafa. Rahoton jaridar The Indian Express ya bayyana cewa maharan sun harba harsasai biyar kan motarsa, yayin da Shroff ya tsira ba tare da samun raunin harbin ba.

Sai dai harin bai wuce ba tare da jikkata wasu ba. Direban jarumin ya samu raunin harbi a hannunsa na hagu, yayin da wani mutum da ke kusa da motar shi ma ya jikkata. An kai waɗanda suka ji raunin asibiti domin samun kulawar likitoci.

Abin da ya ƙara ɗaukar hankalin jami’an bincike shi ne zargin cewa maharan sun san tsarin zirga-zirgar jarumin. A cewar rahoton, Shroff ya kan je wurin domin buga ƙwallon ƙafa a ranakun Lahadi, kuma ’yan sanda na zargin cewa maharan sun yi amfani da wannan masaniya wajen jiran zuwansa. Bayan harin, sun tsere a kan babur, wanda daga baya aka gano a kusa da tashar jirgin ƙasa ta Andheri West.

Binciken kyamarorin tsaro ya taimaka wajen gano hotunan wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a harin. Jami’an tsaro sun kuma kafa tawagogi 15 domin bin diddigin hanyoyin da maharan suka bi, gano masu alaƙa da su da kuma tantance ko sun yi amfani da jirgin ƙasa ko wasu ababen hawa wajen tserewa. Har zuwa rahoton The Indian Express na ranar 19 ga Oktoba, ba a tabbatar da kama waɗanda ake zargi ba.

By ukarofi

Leave a Reply