Bankuna sun nemi masu neman canji su fara bin layi wata guda kafin buƙata

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da canjin kuɗaɗen ƙasar waje suka yi matuƙar wahalar gaske, Bankuna sun umarci masu neman sayen kuɗaɗen ƙasar wajen da su fara bin layin neman kuɗin tun wata guda gabanin lokacin da za su yi amfani da kuɗin. 

Bankuna sun ba da sanarwar tun a watan Mayun shekarar nan da muke ciki ta 2022. Bayan da wasu ɗalibai da kuma ‘yan kasuwa suka yi ta ƙorafin yadda aka ja dogon lokaci kafin su samu canjin kuɗaɗen duk kuwa da sun cika dukkan sharuɗɗan da suka kamata. 

A wata wasiƙa da wata majiya ta bayyana mana, Bankin Access ya bayyana cewa, yana buƙatar waa’adin kwanaki 30 domin samar da canjin kuɗaɗen ƙasar waje don biyan kuɗin makaranta, hayar gida kuɗin kula da kai (A ƙasar waje) ga masu buqatar hakan. 

Hakazalika, shi ma shirya canjin kuɗi don guzurin tafiyar ɗaiɗaikun mutane (PTA), da kuma guzurin ‘yan kasuwa (BTA), su ma za su iya ɗaukar mako biyu kafin a kammala haɗa wa mutum. 

Hakazalika, a dai cikin wasiƙar ta bankin access, an aike da dukkan bayanai da takardun da ya kamata a cike domin cika sharuɗɗan sayen canjin kuɗaɗen ƙasar wajen. Ko da mutum ma ya nema tun kafin wata gidan, dole sai ya cika waɗancan sharuɗɗan sannan zai iya samu.