Bai kamata iyaye su riƙa janye ƙararrakin fyaɗe daga kotuna ba – Shugabar FIDA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugabar Ƙungiyar Lauyoyi Mata ta Nijeriya (FIDA), Aisha Muhammad, a ranar Laraba, ta yi fatali da yawan janye ƙarar fyaɗe daga kotuna da wasu iyaye su ke yi a Nijeriya.

Da ta ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya yayin wata ziyara da ya kai Kaduna, Aisha ya bayyana cewa, ƙungiyar na karɓar ƙararrakin fyaɗe a kullum, inda ta ƙara da cewa, amma yawancinsu an janye su kafin su kai ga kotu.

A cewarta, galibin iyaye suna tsoron wulaƙancin da ’ya’yansu za su iya fuskanta a lokutan aure, don haka su ke janye irin waɗannan shari’o’in idan sun riga sun shiga kotu ko ma kafin su kai ga kotun.

Ta ƙara da cewa, irin wannan abu ba zai haifar da samun adalci ga waɗanda abin ya shafa ba, sai dai ma hakan ya ƙara ƙarfafa masu laifin.

Aisha ta yi kira ga iyaye da su taimaka wajen ƙarfafa wa ’ya’yansu a lokacin da ake kai ƙarar fyaɗe a ofisoshin ’yan sanda tare da tabbatar da cewa ba a janye irin wannan shari’ar ba kafin su kai ga kotu.

Ta ba da tabbacin cewa, ƙungiyar za ta ci gaba da taimakawa wajen kare haƙƙin mata da ƙananan yara har ma da maza, inda ta jaddada cewa, “wasu mazan suna zuwa ofishinmu da ƙorafe-ƙorafensu kuma muna sauraronsu.

Shugaban ƙungiyar ta bayyana cewa, aikin ƙungiyar ya fi kare haƙƙin mata da ƙananan yara, musamman a kan batutuwan da suka shafi rikicin gida, fyaɗe, aikin yara da aurar da yara da dai sauransu.

Ita ma a nata jawabin, Sakatariyar ƙungiyar, Funke Bamikole, ta yi kira ga NAN da ta taimaka a ko da yaushe wajen wayar da kan jama’a ta hanyar da suka dace domin taimakawa FIDA wajen fafutukar kwato haƙƙin yara da mata.

Bamikole ta bayyana jin daɗinsa da haɗin gwiwar da aka yi tsakanin FIDA da NAN wajen tabbatar da adalci ga yara da ƙananan yara.

Manajan shiyya na NAN a Kaduna, Abdullahi Salihu, a lokacin da ya ke maraba da wakilan FIDA, ya yi kira gare su da su jajirce wajen tunkarar ƙalubalen da ke gabansu, kada su yi ƙasa a gwiwa wajen gudanar da al’amuran da ake buƙata wajen samun adalci.

Salihu ya ba su tabbacin ci gaba da yin haɗin gwiwa da NAN, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta kuma taimaka wajen yaɗa bayanan da suka dace ga jama’a.