Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja
A Juma’ar da ta gabata wata ƙungiyar Musulmi daga yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya ta ƙaddamar da Alƙur’anin da ta fassara zuwa harshen Ibo.
Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ta ‘Ibo Muslims D’awah Group’, Malam Muhammad Muritala Chukuemeka ne ya bayyana hakan a ziyarar girmamawa da ƙungiyar ta kai wani kamfanin jarida da ke Abuja ranar Talata.
“Yanzu haka muna da kwafi 500 na wannan fassarar Alƙur’ani, kuma mun aika guda 100 zuwa yankin Kudu maso Gabas domin ci gaba da aikin da’awa ga ’yan uwanmu ’yan ƙabilar Ibo, don haka ina kira ga sauran al’ummar Musulmi da su yi koyi da hakan domin qara yaɗa addinin Allah”, inji shi.
Ya bayyana cewa, shi da sauran ’yan uwansa da ke ƙungiyar sun yi silar musuluntar al’ummar Ibo da dama ba ya ga aikin tarjamar Alƙuranin da suka shafe shekara biyar suna yi.
Malamin wanda haifaffen garin Orlu ne da ke Jihar Imo, ya yi kira ga al’umma da su ɗaure su halarci bikin ƙaddamar da A’lkuranin da za a yi bayan Sallar Juma’a a Masallacin Ansaruddeen da ke Unguwar Maitama a Abuja.
Ya kuma yi kira ga Musulmin Nijeriya da su zauna lafiya da juna, domin kuwa Musulinci addinin zaman lafiya ne da ya haramta kisan ba gaira ba dalili.
