Adalci shi ne mafita ga rashin tsaro

Ganin yadda ake jingina hare-haren ‘yan bindiga akan makiyaya a Nijeriya, ya sa wasu manyan ƙasa suka kafa wata sabuwar ƙungiyar kare harkokin makiyayan da ake kamawa ba tare da laifin komai ba.

Sai dai sabuwar ƙungiyar mai suna ‘Nomadic Rights Concern’ a Turance ba za ta kare waɗanda ke cikin harkar varna da fasadi ba.

Sabuwar ƙungiyar makiyayan da ta yi taron ta na farko a Kaduna, ta ƙaddamar da sabbin shugabannin ta kuma ɗaya daga cikin iyayen ƙungiyar, Dr. Ahmed Mahmud Gumi, ya ce, ƙungiyar adalci za ta tabbatar domin samun zaman lafiya a Nijeriya, ba nuna banbanchin ƙabila ba.

Dr. Gumi ya ƙara da cewa, an ƙirƙiri sabuwar ƙungiyar makiyayan ne don bambance baragurbi da mutanen ƙwarai wanda hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a Nijeriya.

Ya ce, ƙungiyar za ta yi amfani da lauyoyi wajen ganin duk makiyayin da aka kama shi ba tare da haƙƙi ba, ta karvo mai haƙƙin shi, waɗanda kuma aka tabbatar sun yi laifi za ta taimaka wajen hukunta su.

Babban Sakataren ƙungiyar Fulanin Nijeriya da ake kira Gan-Allah Fulani ‘Development Association’, Alhaji Ibrahim Abdullahi na cikin iyayen wannan sabuwar ƙungiyar makiyaya, kuma ya ce, idan ana son samun zaman lafiya sai an gane cewa matsalar tsaro ba daga ƙabila ɗaya ta ke fitowa ba.

Alhaji Abdullahi ya ce, cikin harkar ‘yan bindigan da ke sace mutane akwai Hausawa da Yarabawa da Inyamurai da Fulani da ma sauran ƙabilu saboda akwai masu kai musu makamai da kwayoyi da kuma ɗaukar kayan da su ka sata.

Fulani mata da maza daga yankunan Nijeriya daban-daban ne dai su ka haɗa wannan ƙungiya kuma sun ce za su bi dukkan dokokin ƙasa wajen gabatar da ayyukansu.

Allah ya sa mu dace.

Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, Ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.