
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya caccaki masu sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen zargin ta da rashin aiki yadda ya kamata, yana mai bayyan masu irin haka a matsayin waɗanda suka gurɓace a siyasance kuma suka makance ga ganin nasarorin da ake samu.
A lokacin da ya ke magana a yayin ƙaddamar da ayyukan tituna a yankin Ushafa-Bwari a Abuja, Wike ya ce masu furta waɗannan kalaman mutane ne da suka yi ta tsalle daga jam’iyya zuwa jam’iyya tun daga 1999 kuma suka gaza cin nasara a siyasance.
Wike ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana aiki tuƙuru ta yadda duk inda suke suna ganin ayyukansa, yana mai cewa ba sai an je gidajensu ba kafin su ga ana aiki.
Taron ƙaddamarwar ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu, inda za a yi aikin titunan, waɗanda za su karaɗe hanyoyin Kwalejin Yaƙi na sojoji da wasu wurare a yankin Ushafa-Bwari dake birnin.
Ministan ya kuma yaba wa ƴan kwangilar da ke gudanar da ayyukan da kodinetan ayyuka na Abuja bisa sauke nauyinsu cikin inganci.
Ya kuma ce, aikin wani ɓangare ne na faɗaɗa cigaba a yankunan da aka yi watsi da su a Abuja.
