Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya kan ƙarin kasafin biliyan N895

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Ahmad Lawan, ya karanta wa majalisa wasiƙar da Shugaba Ƙasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar yana neman amincewarta kan ƙarin kasafin kuɗi na biliyan N895.

Lawan ya karanta wasiƙar Shugaban Ƙasar ne yayin zaman da majalisar ta yi a Talatar da ta gabata.

Da ma dai kafin wannan lokaci, Majalisar Zartarwa ta yi na’am da ƙarin kasafin da Buhari ya nema.

Bayanai sun nuna za a yi amfani da wani kaso mai tsoka daga kasafin wajen sayo wa sojoji ƙarin kayan aiki domin ƙara musu ƙarfi wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan fashin daji.

Har wa yau, daga cikin kasafin ana sa ran sayo allurar rigakafin korona gami da magance wasu buƙatu masu alaƙa da sha’anin kula da lafiya.