Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta tsame hannun ministoci daga sabuwar dokar mai

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Talatar da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya aike wa da Majalisar Dattawa da wasiƙa inda ya nemi su yi wa wata sabuwar doka da suka yi ta man fetur (PIA) kwaswarima. Wadda ta ƙunshi cire ministan kuɗi da na albarkatun man fetur.

A cikin ɗaya daga cikin wasiƙun wacce Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zauren majalisar, Buhari ya buƙaci a yi garambawul ga dokar ta PIA, sannan kuma a cire ministan kuɗi da na albarkatun man fetur daga kwamitin na Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPC).

Inda shugaban shi ma da kansa ya nemi a cire shi a cikin ‘yan kwamitin na NNPC a matsayinsa na Ministan albarkatun man fetur.

Ya ƙara da cewa, waɗancan ministoci za su iya ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da dole sai sun kasance mambobi na kwamitin NNPC ɗin ba.

Sannan kuma wata kwaskwaimar da Buhari ya nema a yi wa dokar man fetur ɗin na PIA. Shi ne, a ƙara yawan mambobinta waɗanda ba sa daga hukumar zartarwa a NNPC a waɗanda a halin yanzu suke guda 2, ya nemi a ƙara yawansu su zama shida domin samun wakilci mai kyau.