Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Edita kan lamuran siyasa na kafar watsa labarai ta ‘Arise’, Sumner Sambo yayi la’akari da cewar, ƙetarawar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyar dake riƙe da ragamar mulkin tarayya ta APC ba tare da amincewar tutar kwankwasiyya da jagoranta, Rabi’u Musa Kwankwaso ba, ya zame wa Shugaba Bola Tinubu ala-ƙaƙai.
Kafar yanar-gizo ta ‘Naija on point’ ta ruwaito cewar, Sambo yayin da yake yin tsokaci a shirin na talabijin mai taken “Arise Television’s Morning Show”, ya lura da cewar, hankalin Shugaba Tinubu ya karkatar ne kaco kam akan farin jini da tsarin Kwankwasiyya fiye da tagomashin siyasar Gwamna Abba Yusuf.
Kamar yadda Sambo ya lura, sabagogin siyasar Kano ta sanya Gwamna Yusuf cikin halin tsaka mai wuya, yana mai cewar, matuƙar ba guguwar kwankwasiyya ce tayi wa gwamnan jagorancin canjin sheƙa ba, maƙasudun siyasar sa za ta fuskanci ƙalubaloli nan gaba.
Sambo ya kuma yi nuni da cewar, yin rajista kan fasahar E wa mambobin jam’iyar APC ya samu jinkirin sati guda ne bisa umarin bai wa gwamnan dama ya fara yin rajista, a matsayin mai zamowa shugaban jam’iyar a Jihar Kano.
Ya ƙara da cewar, an kuma ƙalubalanci gwamnan na Kano ya gwamatsi Rabi’u Kwankwaso da zummar shawo kansa zuwa ƙetarawa jam’iyar APC.
Sambo yace, “Idan an taɓo batun Kano, wani lamarin annashuwa ne ke gudanar. Ina kuma iya shaida maka cewar, wani lamari na gagara badau wa Gwamna Abba Yusuf, saboda ta kai ga shi kansa Shugaba Tinubu yana fahimtar yadda takun saƙar take a halin yanzu.
“Kuma wannan tirka-tirkar ce ta sanya yasa shi karan-kansa Shugaba yake shakkar canjin sheƙar Abba Yusuf zuwa jam’iyar APC, saboda matuƙar kwankwaso bai bayar da Kai bori ya hau ba, siyasar Abba tana cikin babbar ƙalubale.
“Za’a samu ƙalubale. Saboda dalilin da ya sanya Tinubu ya zawarci gwamnan, ba wai don karin sa bane shi kadai, saboda tawagar kwankwasiyya ce gundarin ta, bisa jagorancin shugaban ta”, Kwankwaso, domin yin hakan ya baiwa Gwamna Abba damar tarkata tarukucen Jihar ta Kano zuwa jam’iyar APC.
“Kawo wannan lokaci dai, lamarin ya kasancewa Shugaba Tinubu banbarakwai, da ya fahimci hauma-haumar. Kada fa a mance, batun rajistar ‘yan jam’iyar APC a Kano bisa fasahar kimiyya wanda ya kamata ace ya kan-kama tun-tuni, la’akari da cewar, Shugaba Tinubu ne yace a bai wa gwamnan dama ta sati guda domin ya kimtsa yin rajistar tukun, a yayin da kuma aka bashi zarafin ya gwamatsi shugaban na kwankwasiyya, Rabi’u Kwankwaso ya motsa aniya.
“Amma Kuma kawo wannan lokaci, Kwankwaso yana cikin inda-indar motsawa, lamarin da yake jinkirta fara yin rajistar ‘ya’yan jam’iyar ta APC bisa fasahar kimiyya, da fatar Gwamna Yusuf zai yi amfani da wannan katantomiyar ya rinjayi Kwankwaso zuwa masheƙa, kuma matuƙar Abba bai yi haka ba, yana ruwa”.
