
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake ƙasa da sa’o’i 24 da Gwamnan Jihar Ribas ya janye dag takarar gwamna a zaɓen 2027, wani ɗan siyasa da ke amsa sunan Fubara, ya shiga takara a ƙarƙashin tutar jam’iyyar NDC.
Sabon ɗan takarar mai suna Blessing Fubara Snr., ya yanki fom ɗin shiga takarar ne a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, ranar Laraba.
Duk da cewa Blessing Fubara da Gwamna Siminalayi Fubara ‘yan Ƙaramar Hukumar Opobo/Nkoro ne na Ribas, ba a tabbatar da ko alaƙar tasu ta kai tsaye ba ce ko akwai shamaki.
Shugaban jam’iyyar NDC na jihar, Hon. Success Jack ya tabbatar da cewa Blessing Fabarairu ɗaya ne daga cikin ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar, amma ba zai iya tabbatar da ko akwai alaƙar gida ɗaya tsakanin sa da gwamnan ba.
Makonni biyu da suka gabata ne Blessing Fubara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa NDC.
