Da gudunmawar maigidana na zama Hasken Fadar Laƙanin ƙasar Hausa — Sayyada Khadija

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Sabuwar Hasken Fadar Laƙanin ƙasar Hausa, Sayyada Khadija Inuwa Nasir, ta bayyana cewa gudunmawar da mijinta ya bayar da goyon baya da amincewa ne suka zama silar naɗin da aka yi mata a masarautar Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa, Malam Salisu Liman.

Sayyada Khadija ita ce mace ta farko da aka naɗa a matsayin Hasken Fadar Laƙanin ƙasar Hausa. Ta bayyana hakan ne jim kaɗan bayan bikin naɗin sarautar da aka gudanar a makon da ya gabata a Kano.

Ta ce naɗin nata wata falala ce daga Allah, inda ta bayyana lamarin a matsayin abin al’ajabi da ya tabbata cikin ikon Ubangiji. Ta kuma yabawa Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa, Gwani Liman, bisa hikimar zaɓar mutane masu kishin al’umma domin su bayar da tasu gudunmawa wajen cigaban Hausawa.

Sabuwar Hasken Fadar ta kuma jaddada muhimmancin biyayya da haɗin kai a tsakanin ma’aurata, tana mai cewa zaman lafiya a gida shi ne ginshiƙin gina tarbiyyar ‘ya’ya nagari masu amfani ga al’umma da ƙasa baki ɗaya.

A ƙarshe, ta yi kira ga al’umma da su ƙara yawaita addu’a, taimakon marayu da masu ƙaramin ƙarfi, tare da karrama baƙi da maƙwabta, musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan.

By ukarofi