Da yawan magidanta a Nijeriya ba su ne mahaifan ‘ya’yansu ba – Masanin DNA

Daga BASHIR ISAH

Binciken masana kimiyyar ƙwayar halitta (DNA) a Nijeriya ya nuna cewa, magidanta da dama a ƙasar ba su ne mahaifa na asali na ‘ya’yan da ke gabansu ba alhali ba su san da haka ba.

Alƙaluman masanan sun nuna daga gwajin DNA da ake gudanarwa, akan tarar 6 daga cikin kowane yara 10 daga aka bincike su mahaifin da suke ƙarƙashinsa ba shi ne ya haife su ba, wato dai ‘ya’yan wani ne ko wasu ne can daban.

Abiodun Salami ƙwararre ne a fagen sanin kimiyyar halitta daga jihar Legas, ya bayyana cewa kusan kashi 60 cikin 100 na gwajin DNA da sukan gudanar kan nuna saɓani, wato ba a samun daidaiton ƙwayar halitta na yaran da ubanninsu.

Gwajin DNA, gwaji ne da akan yi wanda kan taimaka wajen tantance asalin iyayen yaro don magance zargi a tsakanin ma’aurata da makamancin haka.

A cikin zantawar da jaridar Premium Times ta yi da shi, Salami ya ce daga cikin dalilin da kan haifar da yin gwajin DNA, har da ƙoƙarin gano asalin mahaifan yaro a lokacin da mutum ya yi ƙoƙarin ƙetarawa da yara a filin jirgin sama.

Ya ce idan kuwa ke mace ce, sannan kika buƙaci yin tafiya zuwa ƙetare kina ɗauke da yaro ɗan ƙasa da watanni shida da haihuwa, a nan ma jami’an filin jirgin sama za su buƙaci a yi gwajin DNA don gaskata ɗan nata ne ko saɓanin haka, don yaƙi da matsalar safarar ƙananan yara.

Salami ya ƙara da cewa, sukan yi gwajin DNA don tabbata da asalin mahaifiyar yaro. Sai kuma wani babban dalin da ya ce shi ne, yayin da ake da shakku kan wata haihuwa da mace ta yi ko ciki da ta ɗauka a tsakanin ma’aurata.

Ya ce sun sha cikin karo da batutuwa inda bayan mutum ya shafe shekaru masu yawa yana kula da yaro ko yara a zatonsa ‘ya’yansa ne, amma a ƙarshe sai ya fahimci ashe ba shi ne asalin uban yaran ba sakamakon gwajin DNA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *