
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta dakatar da ɗaya daga cikin mambobinta mai suna Mista Steve Osuji bisa saɓa wa dokar hana bayyana bayanan sirri na dokokin aikin jarida.
A sanarwar da ke ɗauke da sanya hannun Shugaba da Sakataren ƙungiyar, Eze Anaba da Onuoha Ukeh suka fitar, ƙungiyar ta ce akwai yarjejeniyar cewa jawabin da Darakta-Janar na ƴan sandan farin kaya (SSS), Aeola Oluwatosin Ajayi ya yi a taron Bennial Convention karo na 25 a Enugu ba na yaɗa wa al’umma ba ne.
Ƙungiyar ta ce duk da haka, saidai babban ɗan jaridar, Osuji ya wallafa shi a matsayin rubutaccen saƙo a shafukansa na sada zumunta, lamarin da ya zama saɓa wa dokar.
Akan haka ne ƙungiyar ta sanar da dakatar da shi na tsawon shekara guda daga yanzu.
Ƙungiyar ta kuma bai wa Daraktan da hukumar SSS haƙuri bisa tozarcin da mamban nata ya yi sanadin faruwarsa.
Kazalika ta ce, dakataccen mamban yana da damar ɗaukaka ƙara akan hukuncin da ta yanke masa.
