DSS ta cafke Editan Jaridar Al-Mizan, Ibrahim Musa

Jami’an DSS sun cafke Babban Editan Jaridar Al-Mizan, Malam Ibrahim Musa a Babban Filin Jirgin Saman Kano.

Majiyarmu ta ce an kama Musa ne da safiyar ranar Laraba a hanyarsa ta zuwa Saudiyya don Hajjin Umara.

Jaridar Al-Mizan mallakar Ƙungiyar Harkokin Musulunci ta Nijeriya (IMN) ce wadda aka fi sani da Shi’ia.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun Abdullahi Usman, ta ce ‘yan uwan Musa sun yi kira da a sako shi ba tare da wani jinkiri ba.

A cewar sanarwar, “Hukumomi ba su ba da dalilin kama Musa ba duk da dai cewa shi ɗin ɗan sahun gaba ne wajen kira da a sako Sheikh Ibraheem Zakzaky wanda gwamnati ta tsare shi tun 2015 a Jihar Kaduna.

“Ibrahim Musa na tare da wata ‘yar uwarsa, Binta Sulaiman ne a lokacin da jami’an DSS suka ɗauke shi a Babban Filin Jirgin Sama na Aminu Kano da sanyin safiyar Laraba yayin da yake ƙoƙarin zuwa Saudiyya don Hajjin Umara.”

Usman ya ce Ibrahim Musa na daga cikin masu magana kan “matsalar ta’addanci da kisan gilla da kuma danniyar musulmi” da gwamnatin Nijeriya ta yi a ƙarƙashin tsohon Shugaban Muhammadu Buhari.

“Muna fata Shugaba Bola Tinubu ba zai bari ya sifatu da ci wa dimokuraɗiyya dunduniya, take haƙƙin ɗan’adam, kisan gilla ba kamar yadda gwamnatin da ta shuɗe ta aikata,” in ji shi.