In rabonka ne zai zo har gabanka ne

Manhaja logo

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Taken wannan rubutun nawa ya fito ne daga baitukan wata waƙa da wani mawaƙin Hausa hip hop ɗan Jihar Gombe mai suna S. Nigga ya gabatar a gaban dafifin mahalarta taron Tedx Pantami, wanda wasu matasa a jihar suka shirya da nufin tattauna wasu matsaloli da suka addabi al’ummar Arewa, musamman mazauna Jihar Gombe. Har wa yau kuma a samar da mafita wanda gwamnati da al’umma za su yi aiki da su, don samar da canji a rayuwarsu.

Taron, wanda nima na samu damar halarta a matsayin gayyata ta musamman daga masu shiryawa, ya samu halartar manyan manazarta, malaman jami’o’i, da ƙwararru a ɓangarori daban-daban, da suka haɗa da ɓangaren lafiya, ilimi, da zamantakewa. Kuma kowannen su ya gabatar da laccoci da bincike masu kama hankali da zaburar da matasa zuwa ga himmatuwa wajen ba da gudunmawa ga cigaban al’umma, da samarwa kansu kyakkyawar makoma, don gobensu da ta ’yan baya ta yi kyau.

Na kuma samu damar nishaɗantuwa da kalmomin hikima da aka zayyana su cikin waƙe da azanci, waɗanda kuma suka tavo wasu muhimman batutuwa na rayuwa, musamman ga cigaban rayuwar matasa, da kyautatuwar shugabanci a Nijeriya. Daga ciki har da wannan waqa da S. Nigga ya gabatar wacce ba ni kaɗai ba, na lura ta tava mutane da dama, har da farfesoshi da na ga suna sauraron kalmominsa cikin natsuwa, suna ɗan rubuta wani abu a takarda, tare da jinjina kai.

Kalmomin da waƙar ta ƙunsa ba wasu sabbin kalmomi ba ne, waɗanda aka saba ji ne daga bakin masana ilimin ƙarfafa gwiwa da zaburarwa, amma waƙar ta kasance tunatarwa ce da kuma hannunka mai sanda ga matasa, masu zafin nema da burin samun arziki dare ɗaya ko ɗaukaka da shahara. S. Nigga ya tuna musu cewa, in rabonka ne, zai zo har gabanka ne!

Babu shakka kamar yadda muka sha jin ana faɗa zafin nema ba shi ne yake kawo samu ba. Kodayake ba lallai ne kowa ya yarda da hakan ba, akwai masu tunanin cewa ba a kama zomo daga zaune, dole sai an bi shi da gudu an jajirce don a cimma sa. Lallai jajircewa muhimmin mataki ne na samun nasara a rayuwa, kuma duk abin da ka ke nema sai ka yi da gaske wajen nemansa, ka yi aiki tuƙuru, tare da bin matakan da suka dace.

Babu ma kamar yanzu a irin wannan lokaci da rayuwa ta yi tsada, rashin tabbas a rayuwar ’yan Nijeriya ya ƙara yawa. Kullum mutum ya tashi sai ya ga sabbin abubuwa masu rikitarwa da ɗaure kai. Kama daga farashin kaya a kasuwa, canjin farashin abin hawa na sufuri, daga gida zuwa wajen aiki ko kasuwa. Ƙarin kuɗin makaranta da kuɗin haya.

A daidai lokacin da nake wannan rubutu ƙungiyar ma’aikata ta NLC da ta ’yan kasuwa TUC na cigaba da tattaunawa da gwamnati game da batun tafiya yajin aiki, saboda matsin lamba wa Gwamnatin Tarayya don ta samar da wasu tsare-tsare da za su sassautawa ma’aikata ƙuncin rayuwar da suke ciki, musamman ma batun ƙarin albashi, da biyan tallafin da gwamnati ta yi alƙawari, na tsawon watanni shida, da sauran alƙawuran da har yanzu babu wanda aka fara cikawa.

Sannan ga batun zanga-zangar da ɗalibai ke yi a wasu jami’o’in ƙasar nan dangane da batun ƙarin biyan kuɗin makaranta, wanda ’yan Nijeriya da dama ke kokawa a kai. Suna bayyana cewa karatun jami’o’in gwamnati sun fara gagarar ɗan talaka, saboda tsadar da ilimi ke ƙara yi.

Waɗannan abubuwa da ke faruwa a ƙasar nan na daga cikin dalilan da ake dangantawa da musabbabin ƙaruwar ayyukan ta’addanci da ƙananan laifuka a cikin al’umma irin su sace-sace, ƙwacen waya, fashi da makami, garkuwa da mutane, karuwancin ’yan mata da matan aure a ɗakunan mazajensu, da ’yan mata a makarantu, da sansanonin ’yan gudun hijira.

Duk saboda talauci da tsadar rayuwa da suka jefa ’yan Nijeriya da dama cikin rashin tabbas da rashin madogara. Wasu rahotanni da BBC Hausa ta fitar sun yi nuni da yadda wasu ‘yan Nijeriya ke dafa ruwan zafi su sha don rage kaifin yunwa, sakamakon rashin abin da za su sayi abinci, ko su kula da iyalinsu. Mata da maza masu lafiya sun cika gari da tituna suna yawon bara su da yaransu, don su samu abin da za su sa a bakunansu.

Ko waɗannan fitintinu kaxai sun isa su sa mutum rikicewa da fita daga hayyacinsa, don rashin sanin me gobe za ta haifar masa shi da yaransa. Don haka mawaƙan zamani irin su S. Nigga ke tambayar mece ce makomar ƙasar nan? Ina matasan ƙasar nan za su sa kansu? Wacce gudunmawa za su bayar da za ta kawo sauyi ga halin da Arewa da sauran sassan Nijeriya ke ciki?

Amsoshin waɗannan tambayoyi dai na tare da mu. Kada mu bari halin da muke ciki a yanzu ya rufe mana ido mu kasa hango gobenmu. Kada mu bari mutuwar zuciya ta kashe mana gwiwa mu kasa zagewa mu nemi sana’o’in dogaro da kai, mu nemi ilimi, mu shiga kasuwanci iri-iri da ake da su, musamman ilimin fasahar zamani, da na ƙirƙira da dabarun ayyuka da cinikayya ta yanar gizo, wanda matasa a manyan ƙasashen duniya ke cin moriyarsu, domin mu fita daga halin da muke ciki, kuma mu kawo sauyi a rayuwarmu da ƙasar mu baki ɗaya.

Kada mu ɗauka halin da muke ciki mai ɗorewa ne, a’a, sam. Da izinin Allah muna da kyakkyawan zaton nan da wani taƙaitaccen lokaci za a samu sassauci, talaka zai sha iska daga shaƙar da talauci ya yi masa. Darajar kuɗin ƙasar mu za ta dawo, farashin kayan masarufi da sauran hidimomin rayuwa za su sauka ƙasa sosai.

Amma fa sai mun miƙe mun yi da gaske wajen kawo wa rayuwar mu, mu tuna fa babu maraya sai rago! Mun dai ga irin tallafin da ake cewa gwamnati na bayarwa da yadda yake zirarewa ta hannun wasu ’yan tsiraru, an bar talakawa da shinkafa gwangwani da taliya ƙwaya ƙwaya. Kada mu zauna jiran samun taimako daga wajen wani, mu nema a wajen Allah kawai, mu kuma himmatu wajen ganin ƙasar nan bata durƙushe gabaɗaya ba.

Ba sai mun nuna hassada ko baƙinciki ga abin da wani ke da shi ba. Ko mu riƙa zargin wani akan makircinsa ko sharrinsa ne ya sa ba mu samu wani abu ba. In dai muka tashi muka nema, za mu samu daga arzikin Ubangiji. Kuma ka tuna, in rabonka ne, zai zo har gabanka ne. Amma ba daga zaune ba, ba daga yawon maula, ko shaye-shaye ba!