Da me matan banza suka fi na gida?

Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafin zamantakewa a jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Yau zan so mu tattauna wani batu mai matukar mahimmanci, wato dame matan banza su ka fi matan cikin gida? Wannan tambaya ce da matan aure kan yi wa mazaje don gano dalilin da ya sa suke bin matan banza. Bayan ga su nan a gida, ba abinda suka rasa na halitta ko kyautatawa. Gaskiyar magana, da yawa matan waje sun fi na cikin gida ta fuskoki da dama. A biyo ni a hankali don tattauna waɗannan batutuwa:

  1. Kwalliya/Ado: Matan waje ba su da iyaka, idan Magana ake ta kwalliya. Za su kashe kudi ko nawa don suyi adon da zai ja hankali. Sannan kuma, suna iya samun tallafi na kuji daga wajen wasu mazan da yawa. Don haka siyan kayan ado ba wani babban abu ba ne a gurin matan waje.

Ita kuma matar gida mafi akasari idan aka auro ta aka mata kayan lefe, toh shi ke nan. Wata kafin ta kara ganin irin wannan hidimar sai a shekara goma, sai dai idan zai kara aure, shi ma kuma ba kowa ba ne yake yi. Maza da yawa ba sa iya kulawa da wannan hidimar. Kuma idan ba ka yi ba, to wa zai yi mata? Da kafin aure tana iya yi, saboda ba kai kaɗai ne kake zuwa neman ta ba, don haka, kowa yana iya mata hidima. Iyayenta su yi, samarinta su yi. Bayan aure, wannan ba zai samu ba. kuma shi ya sa ita ta cikin gidan ba za ta taɓa burge ka ba, kamar yadda na wajen za su burge ka. Saboda ka riga ka kashe ta da wahala, Don haka, shi ya sa kake fita waje ka nemi matan banza.

  1. Gyaran jiki: Haka gyaran jiki. Matar banza ko nawa ne za ta iya kashe wa kanta don ta yi tsaf-tsaf, sai ka ga fatar mace kamar fatar jariri saboda gyara. Haka nan idan ta ga alamun kayan aikinta sun fara samun matsala, sai ta ruga ta sayo kayan gyara don a musu garan-bawul.

Ita kuwa hajiyar cikin gida, amfana kawai aka iya yi, yara su amfana, kai ma ka amfana, amma ba gyara. Malam, ko mota ka siya ka ajiye idan ba ka mata sabis ba za ta yi qarko ba. Kana ƙorafi jiki ya lalace, nankarwa ko’ina, ga abubuwa duk sun zube. Toh da ka je waje, kuma can ɗin ma kuɗinka za ka bayar ka ji daɗi ƙalilan, ba gwara ka biya kuɗin ka gyara ta cikin gidan ba sai a ci gaba da lallaɓawa, ko ba komai ba ruwanka da tsoron ɗaukar cuta da lalacewar dukiya sakamakon zina.

Uwargida ko da mai gida yaƙi ba ki kuɗi ki gyara jikinki, yana da kyau ki tuntuɓi ‘yan uwanki mata don su koya miki yadda ake sarrafa kayan itatuwa da kayan ganyayyaki wajen gyaran jiki. Tun daga gyaran warin jiki, zuwa gyara mama, zuwa gyaran mazaunai, zuwa gyaran nankarwa, duk akwai hanyoyin gyara su.

  1. Sutura: Tabbas wani ɗinkin sai matan banza. Za su saka maka kaya na wulaƙanci, irin wanda sai ka ji kamar zuciya za ta fita, saboda kwaɗaituwa. Sun san abinda yake birge namiji. Wata akwati gare ta na kayanbacci, kayan wanka da sauransu.

Ke kuma kina gida duk kin boye kaya a akwati, ba kya sakawa sai za ki fita. A nan ne zan ce mata da yawa ba su da dabara. A cikin gidanki ne ake buƙatar kwalliyarki ba sai za ki fita ba. Idan mai gida yana gida dole ki zama cikin ado, ƙamshi, da tsafta. Sannan idan kuka keve, yana da kyau ki saka masa wannan kayan baccin na kece raini ɗin naki. Ya zamana cewa yana gani a cikin gidansa, ba sai ya fita waje ba.

Yana da kyau Alhaji ya sani, su ma wannan matan na waje, kuɗi suka saka suka sayi wannan rantsattsun kayan baccin. Kuma dole daga cikin irin kuɗaɗen da kake ba su. Kullum nakan ce, idan za ka iya bai wa matan banza dubu ɗari, me ya sa ba za ka iya bai wa ta cikin gida dubu ɗari biyar ba? Ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron ranar haɗuwarka da shi.

  1. Aza rum: Ɗaya daga cikin wuraren ƙwarewar na matan banza shi ne, kama zuciyar namiji ta wajen kwanciya. Matar banza tana da lokacin karanta maƙalu ko wasu littattafai, don ta koyi kwanciya iri-iri, don gamsar da abokin harkarta. Haka nan, ta san sanda ya dace ta sha magani don inganta lafiyar can ƙasa-ƙasan.

Ita kuma uwar gida in dai mai gidan yana karva, toh fa ba ruwanta da yana gamsuwa ko ba ya yi. Ba ta san ya kamata ta riƙa gyara wajen ba. Wasu mazan sai ka ji suna cewa, matansu ko sumar gabansu ba sa askewa, sai wajen ya yi ta wari. Sannan ga bushewa. Ba a shan maganin don ƙara ni’ima.

Toh amma ruwa baya wari banza, inji malam bahaushe. Kai Alhaji, wane ƙoƙari kake yi don ganin an gyara? Wasu matan ma da gangan suke ƙin gyara wa saboda ba ka yabawa idan sun yi. Mata kuwa suna son yabawa. Don haka, a riƙa ba ta kuɗi tana siyan kayan gyaran aza rum. Sannan ke kuma uwargida, ki canja salon kwanciya, a zo wa da mai gida sabbin salo don ƙawatar da shi.

  1. Kyan Diri: Shin matan waje sun fi na gida kyan diri ne ko kuwa? Maganar gaskiya sam ba haka bane. Kowa yana da irin halittar sa. Kuma shi diri, abubuwa da yawa suna gyara shi. Na farko shi ne cimar abinci. idan mace ba ta samun kulawa, kuma ba a kulawa da damuwar ta, to kana zaune kana kallon kyan dirin zai tafi, maman ya zube, jikin ya yamushe. Dole sai an yi gyara a wannan ɓangare. Ita matar waje kullum a cikin kula da kanta take, saboda ta haka ne za ta samu kasuwa.
  2. Iya kisisina: Matan waje sun iya kisisina, sun san me namiji yake so. Don haka, za su yi hakuri da kowane irin wulaƙanci don su samu biyan buƙata. Ita kuma matar gida ba wai kisisinar ce babu ba, a’a. Ba za ta yi ba ne. Gani take kisisinar ba ta da amfani. Wallahi ki fara tana ci.
  3. Iya Siyasa: Matan wajen sun iya siyasa. Sun san duk yadda za su tafi da abokan mu’amalarsu. Ba sa bari a yi faɗa. Ke kuma ta cikin gida ba kya iya siyasar aure. Gani kike ai kin isa, sai yadda kika yi. To namiji sai da siyasa, kamar yadda kuma wani lokacin sai da siyasa ake iya maganin ku. Idan matar banza za ta daure da kowane irin wulaƙancin don ta zauna lafiya kuma don kar a rabu da ita, me ya hana ke ma ki yi? Hakuri ta fi ki? duk ba buqata ɗaya kuke karewa ba? A nan za mu dakata, sai mako mai zuwa za mu kammala.

Muhammad Ubale Ƙiru, baƙon marubuci ne a wannan shafi. Muna godiya ƙwarai da gaske.

Imel: [email protected]

Lambar waya: 07087789463