Kotu mai matakai uku, Abba zai shiga uku

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A Hausa in an ce mutum “YA SHIGA UKU” a na nufin ya shiga garari da sai yadda hali ya yi a samu a ceto shi ko ya kuɓuta daga damuwa. In an duba 3 a gurguje ka iya zama duwatsun murhu da duk wanda ya shiga tsakiyar su in ba tukunya ba to zai ji jiki ko za a yi abun nan da a ke cewa “Da kyar na tsira ya fi da ƙyar a ka kama ni.” Amma abun na da ke son magana a nan shi ne damar ɗaukaka ƙara har matakai uku na kotu ga zaɓen gwamna a nan Nijeriya.

Ba kamar a tsarin zaɓen shugaban ƙasa da a ke da dama biyu ba ma’ana daga kan kotun zaɓe da ke zama a kotun ɗaukaka ƙara sai kuma Kotun Koli. Kamar yadda ya faru a sakmakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 inda bayan hukuncin kotun ƙarar zaɓe da ta tabbatarwa Bola Tinubu nasara, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Leba sun garzaya Kotun Koli wacce ta ke ta ƙarshe don neman a rushe zaɓen. Lauyoyin Atiku ƙarƙashin babban lauya Chris Uche sun shigar da ɗaukaka ƙarar don watsi da hukuncin kotun zaɓen.

Uche ya ce sam kotun zaven ba ta yi adalci ba don ba ta duba hujjojin da a ka gabatar ma ta yadda ya dace ba kafin yanke hukunci.

Hakanan lauyoyin sun kawo batun rashin tura sakamako ta na’ura da PDP ke ganin na daga hanyoyin da zaɓen ya zama akwai murɗiya a ciki. Su ma lauyoyin Obi sun shigar da irin wannan ƙarar bayan watsi da hukuncin kotun Haruna Tsammani.

Da yawa daga jami’an gwamnatin Tinubu na ɗaukar ɗaukaka ƙarar zaɓe da manyan jam’iyyun adawa su ka yi bayan hukuncin ƙarar zaɓe da ya ba wa Tinubu nasara aikin babban giwa ne.

In za a tuna kotun ƙarar zaɓe ƙarƙashin Haruna Tsammani ta kori ƙarar jam’iyyar PDP, LP da APM ta ba wa Tinubu na APC nasara.

Tun zaɓen 2003 da tsohon shugaba Obasanjo da mataimakinsa Atiku su ka lashe ba a daina tafiya Kotun Koli ba har yanzu sai a 2015 bayan Jonathan ya fazi zaɓe.

Kalaman tsohon shugaba Buhari a zuwan sa koli na ƙarshe a 2011 na nuna ba ja da baya ga garzayawa kotu.

Mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul’aziz Abdul’aziz ya ce in da ma an samu ɗaya daga alƙalan kotun qarar zave ya ga gaskiyar ‘yan hamayyar da za su iya tsammanin wani tagomashi a kotun koli.

Jigon kamfen ɗin PDP Yusuf Dingyadi ya ce su na sa ran hujjojin su za su gamasar da kotun koli don in ba hakan a ka yi ba, ba a san abun da zai faru nan gaba in an samu zargin murɗiyar zaɓe ba.

A na su ɓangare, kakakin kamfen na Peter Obi na Leba Malam Yunusa Tanko ya nuna akwai dalilai da za su sake gabatarwa da ke nuna shugaba Tinubu bai ma cancanci takara ba. Tanko ya ƙara da cewa ko ba su samu nasarar ƙarar a kotun koli ba, to duniya za ta yi mu su shaidar sun ɗauki matakin da ya dace na ƙalubalantar abun da su ka zayyana da fashi da makami na zaɓe.

Ba a dai yi wa kotu riga-malam, amma a tarihin shari’ar zaɓen shugaban ƙasa ba a taba sauke shugaba a kotun koli ko umurni da a sake zaɓe ba amma an yi a kan gwamnoni da majalisar dokoki.

Ga zaɓen gwamna za a fara daga kotun ƙarar zaɓe da ta ke ta farko. In an yanke hukunci duk wanda bai gamsu ba sai ya ruga kotun ɗaukaka ƙara. A nan ma in an kammala duk wanda bai gamsu ba sai ya nufi kotun koli shikenan daga nan duk hukuncin da a ka yi wanda bai gamsu ba sai dai ya ja Allah-ya-isa!

Na lura da yanda hukuncin kotun ƙarar zaɓe na jihar Kano ya ɗauki hankali fiye da wanda ya faru a Bauchi. Da yawa ma mutane ba sa maganar Bauchi inda kotun ta tabbatarwa gwamnan da ke gado Bala Muhammad na PDP nasara kan wanda ya shigar da ƙara ɗan takarar APC Sadique Abubakar wanda har ila yau shi ne tsohon babban hafsan sama na sojan Nijeriya.

Alƙalai su na da wata dama bisa doka ta yanke hukunci kuma ko da hakan zai yiwa wasu daɗi ko hakan zai ɓatawa wasu rai. Bisa wannan dalili a ke son alƙalai su zama masu gaskiya da amana. Haƙiƙa in an yanke hukunci na gaskiya ba damuwa ko da wani zai ɗaukaka qara. Kazalika ba a yi wa kotu shishshigi gabanin yanke hukunci.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da a ka fi sani da Abba Gida-Gida ya yi watsi da hukuncin kotun ƙarar zaɓe ta gwamnan jihar da ta soke zaɓen sa da ayyana Nasir Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zave.

Tun gabanin hukuncin dama an yi ta yayata yiwuwar samun nasarar Gawuna da kalamai masu nuni da hakan musamman a kafafen yanar gizo.

Gwamna Yusuf ya yi alwashin ɗaukaka ƙarar hukuncin zuwa kotun ɗaukaka ƙara don buƙatar ta dawo ma sa da nasarar sa.

An samu musayar kalamai tsakanin magoya bayan NNPP ko Kwankwasiyya da kuma ‘yan APC da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

A irin wannan shari’ar akwai damar ɗaukaka ƙara har zuwa kotun koli.

Haƙiƙa wannan shari’a ta Kano ta ɗauki hankali ainun don yadda hakan ya shafi lamuran siyasar arewacin Nijeriya.

A yanzu haka a Kano an iyana dokar hana yawo dare da rana don kauda-barar karya doka da oda bayan hukuncin kotun ƙarar zaɓe.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Muhammad Usaini Gumel ya sanya hannu kan takardar umurnin hana yawon bayan ba da damar hakan daga gwamnatin jihar.

Kwamishinan ya ce da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro kuma bisa hurumin rundunar an agyana dokar da gargaɗin duk wanda ya nemi keta haddi zai fuskanci hushin doka.

Tuni a ka baza jami’ai a sako-sakon birnin da girke jami’ai a mashigun birnin don tabbatar da aikin dokar.

Hakan ka iya zama mataki don hana maimaita yanda ‘yan zauna gari banza su ka rufarwa shagunan jama’a a lokacin da a ka ayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

An ga mutane na ta rige-rigen rufe shagunan su don gujewa tabka asara daga masu amfani da irin wannan dama wajen tada zaune tsaye. Tun gabanin ranar yanke hukuncin gwamna Yusuf ya kori kwamishinan filaye Adamu Aliyu Kibiya don samun sa da laifin barazana ga alƙalan kotun zaɓen jihar da kisa.

An lura kalaman na Kibiya sun nuna yadda wasu su ka hakikance sakamakon hukuncin kotun ba zai mara baya ga gwamnatin NNPP ba. Ko a ina su ka samu labarin dai ba mu sani ba amma yanzu tun da an yanke hukunci maganar raɗe-raɗi ta kare.

Gwamnan ta sanarwar kwamishinan labaru Halilu Dantiye ya nesanta gwamnatin sa daga kalaman Kibiya wanda ya ke nuna matuƙar alkalan su ka karvi kuɗi su ka juya hukunci zuwa ba wa “APC” nasara to zai ɗauki matakan gamawa da su da tada fitina a jihar.

Abba Kabir ya ce gwamnatin sa na girmama alƙalai; don haka ya ja layi daga yanzu wajen hana kowa maganganu ba da izini ba.

Gatarin gwamnan bai tsaya nan ba don ya sauka kan mai ba shi shawara kan matasa Yusuf Imam don samun sa da laifin cin zarafin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

Yanzu dai kallo zai koma kan kotun ɗaukaka ƙara da ke Kaduna wacce za ta duba ko shin kotun ƙarar zaɓe ta Kano ta yi daidai ko kuwa a’a. A tarihi a kan samu sauyin hukunci a kotun ɗaukaka qara in ma nan take za a iya misali da shari’ar baya-bayan nan tsakanin gwamnan jihar Osun Adeleke Ademola na PDP da tsohon gwamnan jihar Gboyega Oyetola wanda tuni shugaba Tinubu ya nada a matsayin ministan sabuwar ma’aikatar lamuran teku.

A kotun ƙarar zaɓe Oyetola ya samu nasara inda nan take Ademola ya ɗaukaka ƙara kuma ya samu nasarar soke hukuncin kotun zaɓen. Oyetola bai gaji ba sai ya nufi kotun koli wacce ita ma ta sake ba wa Ademola nasara. Babban abu dai a nan shi ne bin matakan shari’a har karshe kafin saduda a irin wannan yanayi da magoya baya na kowane ɓangare ke marmarin lalle-lalle gwanayensu ne za su dare karagar mulki.

Kammalawa;

Babbar shawara ga kowane ɓangare na siyasar Kano ita ce amfani da hankali wanda haƙiƙa ya fi amfani da agogo. Duk murna ko duk vacin rai jihar Kano ko kuma in ce ƙasar Kano dai ta girmi duk masu hamaiya da juna. Ba wata ribar fito na fito da makamai ko musayar baƙaƙen maganganu a kafafen labaru. A gurguje zan iya lissafa mutum huɗu da sun yi gwamna a Kano a zamanin soja da farar hula amma tuni sun koma ga Allah.

Marigayi Audu Bako, Marigayi Abubakar Rimi, Marigayi Sabo Bakin Zuwo da Marigayi Abdullahi Wase. Abun da na ke son nuni da shi shi ne matuƙar ba a yi tashin kiyama ba bayan dukkan mu ko masu hannu a yanzu a siyasar jihar Kano sun koma gidan gaskiya za a sake yin wasu gwamnonin. Don haka a bi matakan shari’a da kuma matakan addu’ar neman taimakon Allah.