DSS ta kama tsohon ministan Buhari, Hadi Sirika kan gidogar ‘Nigeria Air’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika wanda ya yi amfani da jirgin saman Ethiopia wajen zamba a Nijeriya kimanin Naira biliyan 139.3.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sirika ya isa hedikwatar DSS da ke Abuja domin amsa tambayoyi a wata mota ƙirar Range Rover SUV a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023.

Rahotanni sun ce jami’an DSS sun yi tsare sa na tsawon sa’o’i.

Wannan tuhumar na zuwa ne bayan da muƙaddashin Manajan Daraktan Kamfanin na Nijeriya Air, Captain Dapo Olumide, ya bayyana cewa jirgin da aka ƙaddamar a matsayin Nigeria Air, wani jirgin sama ne da aka yi hayarsa daga kamfanin Ethiopian Airlines.

Olumide ya shaida wa Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin sufurin jiragen sama cewa an yi amfani da jirgin ne wajen ƙaddamar da tambarin jirgin Nijeriya Air amma har yanzu bai fara aiki ba.

Jirgin da aka ƙaddamar da shi an bayyana cewa ya haura shekaru 10 da haihuwa kuma a baya kamfanin jiragen saman Habasha da na Malawi ne ke sarrafa shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *