Duk mai son cin kujerar Gwamnan Kano a 2023 ya ba ni takarar mataimakiya, inji Rashida Maisa’a

Rashida Abdullahi, wadda mutane suka fi sani da ‘Mai Sa’a’, fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood ce da ta daɗe tana jan zarenta; bayan nan kuma ‘yar siyasa ce a Jihar Kano, wanda yanzu haka tana ɗaya daga cikin masu taimaka wa Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a ayyuka na musamman.
A wannan hirar da Manhaja ta yi da ita, ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar mataimakiyar gwamna a jihar idan Allah ya nufe mu da ganin zaɓen 2023. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Daga AISHA ASAS, a Abuja

Za mu so ki fara da gabatar da kan ki.
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Sunana Ambasada Rashida Abdullahi Mai sa’a, kuma jarumar fim, sannan shahararriyar ‘yar siyasa a faɗin Tarayyar Nijeriya.

Kwanan nan mu ka samu labarin za ki yi takara a zaɓe mai zuwa. Shin mene ne gaskiyar wannan maganar?
To gaskiya ita wannan maganar, a kullum jama’a kan ce idan na fito takara zan ci, kuma a inda aka fito ba ni da sha’awar takara, to da na tashi takarar tawa na ce bari in fito takarar ‘Mataimakiyar Gwamna’ saboda ko a hirar da mu ka yi a gidan rediyo ana cewa, mutane su na cewa ko in fito takara, ko kuma in dawo harkar fim, don ana so a dinga ganin ‘movement’ ɗina, sai na ce to bari in fito takarar mataimakiyar gwamna.

Me ya sa ki ka zaɓi takarar mataimakiyar gwamna?
Eh to, abin da ya sa na ce zan fito takarar mataimakiyar gwamna, kin san ba za a ba wa mace takarar gwamnan Kano ba, amma mataimakiya zan samu, domin na san duk ɗan takaran da ya ke son ya ci zaɓe, idan ya haɗa kai da ni, in sha Allahu zai ci zaɓen.

Saboda mu muna harkar sha’ani na al’umma, mu na harkar ƙungiyoyi, kuma muna harkar ‘charity’ na taimakon al’umma, duk inda mu ka shiga. Mu ba kamar sauran ‘yan takarar ba ne, ko ma waɗanda su ka ci. Wani ma idan ya ci zave ba ya zuwa qaramar hukumar shi. Amma ni yanzu a Kano zan iya fitar ma ka da wasu ƙauyuka da dama da wani ɗan takarar ma bai san da su ba. Amma ni a kan harkar ‘charity foudation’ ɗina da na ke yi da kuma na matar shugaban ƙasa da na ke yi na ‘Feacture Assured’ wanda na ke rarraba wa mutane kayan masarufi, da sauran kayayyaki na more rayuwa. Don haka duk in da mu ka ce za mu fito takara, ko mun fito takara, kamar a ce wane kaza zai yi takarar gwamna, Rashida ce mataimakiya, za su zaɓe mu, saboda sun san idan na ci zan yi adalci.

Mutane da yawa za su yi mamaki, a ce kin fito takarar mataimakiyar gwamna, maimakon ki fito gwamna, ko ‘yar majalisa ko sanata, sai kawai a ji mataimakiyar gwamna ki ka fito.
Gaskiya ni mataimakiyar gwamna na ke so, saboda yanzu haka akwai ‘yan takarar da su ka fara kirana, da su ka ga ‘interview’ ɗina a jarida, kusan ‘yan takara biyu sun kirani a cikin ‘yan siyasar mu na Kano, wanda ‘yan takaran gwamna ne, suna son mu zo mu zauna, idan da gaske na ke abin da, na faɗa, mu haxa qarfi da ƙarfe. To ni kuma abin da ya sa na fito takara akwai wata ƙungiya da ta ke a Amurka, wadda ke kin sani matsayin ki na ‘yar jarida, waɗanda za su ɗauki nauyin mata, daga Naira biliyan ɗaya zuwa biliyan ɗari, waɗanda in za su yi takara. Saboda ana son mata su karɓi abin sosai. Mun yi zama a Kano a nan Tahir, kuma mun yi a Abuja ma. Kuma sannan mun yi a Landan ma. Duk mitin ɗin mun yi shi ne a kan gamayyar ƙunyiyoyi na mata ta duniya.
To sai mu ka samu ‘Vice President’ ta Amurika, wato mataimakiyar Biden, ta goyi bayan abin, ko lokacin da mu ka yi zaman na Abuja ta yanar gizo tare da ita mataimakiyar Shugaban Ƙasar Amurika. Ka ga ai shugaban ƙasar ma ba a jin shi, ita ce ake ta ji. Ka ga ni ma idan mu ka ɗauki mai kasala, sai mu tsaya tsayin daka mu yi wa mutanen Kano aiki.

To sai a ga kamar gasa ki ke yi da ita Mataimakiyar Shugaban Ƙasar Amurika kenan?
Ai ba gasa ba ce, ita ta ƙara mana ƙarfin gwiwa, saboda kishin mata da take yi. Akan a fito a zama sanatoci, ‘yan majalisu, gwmnoni a wasu jihohi, a fito mataimakan gwamnoni, duk wani muƙamai da ki ka sani. To ni kawai abin da na yi sha’awa, ba na son in kai kaina nesa, in ce zan yi takarar gwamna, kuma a Kano akwai ‘yan takarar gwamna da na ke jin nauyin su, ba zan iya fitowa takarar gwamna ba. Amma da gwamnan zan fito, duk kuɗin da za a kashe sai mu yi wasar, mu yi ƙoƙarin, kuma mu yi bajintar, kuma sai ki ga idan Allah ya nufa, sai mu samu nasara. Amma gaba zan iya zama gwamnan ai. Gaba dai gaba dai, don ina da yaƙinin duk ɗan takarar da ya haɗa kai da ni, da izinin Allah da darajar Manzon Allah (S.A.W) sai mun mulki Kano 2023. Yadda ki ka yi tattaunawar nan da ni, sai kin shigo har ofis ɗina na ‘Deputy Governor’ kin yi min.

To yanzu ki na ganin al’ummar Jihar Kano, ana cewa Kano tumbin giwa, tushe ne na shari’a, tushe ne na al’ada da sauran su, ki na ganin za su karɓi mace a matsayin jagorar su?
To ai shi ya sa ka ji na ce in fito takarar mataimakiyar gwamna, saboda Kano duk tunanin da ka ke yi sun wuce hakan, lokacin da na yi hira a gidan rediyo, akwai wata jarida, na manta sunanta da ta ɗauki hirar, ta yanki daidai in da na ce zan yi takarar mataimakiyar gwamnan, wallahi na sha kira gur- guri, da ƙungiyoyi, ba irin ƙungiyoyin da ba su kirani sun yi min magana ba. kuma sannan ni Alhamdu lillahi, ina cikin ƙungiyoyin da su kaɗai ma sun isa su yi zaɓe su ci a Kano. Saboda ni ‘yar Tijjaniya ce, kuma na san za a karɓi abu na, kuma za a yi min addu’a, shi ya sa na ce duk wanda Allah ya sa ya na da rabo, ya fito mu haɗa kafaɗa da kafaɗa da shi, ya nemen. Duk ɗan takarar da ya ke son ya ci ya neme ni. Mu zo mu zauna da shi, mu yi yarjejeniya, Idan ya yi shekara huɗu akai, ni ma ya ba ni in yi huɗu. Dama shine dalilina, don ba zai yiwu in zo in haxa kai da kai, kai ka na gwamna, ka ce sai ka kai shekara takwas ba. Amma idan za ka yi harkar ta karɓa-karɓa, kowa ya ɗana. Shi ma wanda zai yi min mataimaki, idan na yi, shi ma zan bar shi ya ɗana.


To me ya sa ba za ki bar shi ya yi shekara takwas ba?
Ni ai ka ga gaskiya burin da na ke da shi, shekara huɗu na ke son in yi, kuma in sha Allahu idan na yi shekara huɗu, wasu huɗun zan iya zama gwamnar Kano alfarmar Manzon Allah. Saboda ni da Annabi na ke gadara da tinƙaho. Kuma na san Allahi zai min don Annabi. Ka ga ai duk abin da mutum ya sa a gaban shi, in dai ya riƙe Allah da Manzonsa ba zai tave ba. Ban taɓa jin ɗar a wannan takarar da zan fito ba, gabana bai taɓa faɗuwa ba. Kullum ina samun ƙarfin gwiwa.

Me ya sa ba ki zaɓi ki fito ‘yar majalisa ba, ko ciyaman ta ƙaramar hukuma ko mataimakiya?
A’a, ka ga idan aka ce ɗan majalisa, wani yanki zan yi, idan aka ce sanata shi ma wani yanki zan fito, amma ni ƙananan hukumomi 24 nake so na mulka. Ka ga ni tun da na fara, a jam’iyar APC ina da muƙamai da yawa na jiha. To ka ga a matsayina ta wadda ke da muƙamai a ƙasa ma, idan aka ji ni Rashida Mai Sa’a na fito takarar mataimakiyar gwamna, in Allah ya yarda wannan jam’iyya ta mu za ta ƙara samun albarka. Domin ko wace jiha a Nijeriya, an sanmu, an san sunan mu. Ka ga zan ba wa mata na sauran garuruwa ƙwarin gwiwa su fito takarar ‘yan majalisu, gwamnoni da ma sauran su. Amma ni daga kan mataimakiyar gwamna na ke so na fara.

To amma kin san kundin tsarin mulki bai ba wa mataimakin gwmna damar ya fito takara shi kaɗai ba, yadda tsarin yake shine; bayan an tsayar da ɗan takarar gwamna a jam’iya ne, sannan zai zaɓo wanda yake so ya yi masa mataimaki. Ba kya tunanin bayan an tsayar da mai takarar gwamna ya butulce ma ki ya je ya ɗauko wani mataimakin, bayan ya gama cin moriyarki wajen neman a tsayar da shi takara?
Ai kafin a yi zaɓen zai yi ‘disappointing’ ɗina ba bayan zaɓen ba ko. To ai zai gani a ƙwaryarsa. Bayan mu ne Kanon. Tabɗi! Ai sai ya riga rana faɗuwa, billahil azimin kin ji na rantse in dai a Kano ne, billahil azim duk wanda ya takamu in dai a siyasa ne sai mun takashi. Duk wani ƙulle-ƙulle da shige da fice da ake, wallahi duk wani abu da aka yi a Kano da ni Rashida Aldullahi mai sa’a aka yi shi, da mu aka dama.

Kina nufin ki ce min da ku aka yi aikin gama?
Ah. Ki je ki tambaya, har yanzu zan iya gaya ma ki akwatina na gama. Ka tambayi ciyaman na Tarauni Habu Zakari Habu, akwatin mu ɗaya da shi. Mu mu ka fara akwatin mu, kafin a ce komai an gama. Ka san ko tun da har aka ɗauki akwati aka ban na zo na shiga na fita aka ci zaɓe a gama na ke maki magana ba a Tarauni ba, kuma Municipal na je zaɓen Sha’aban Sharaɗa, muka kayar da wanda yake kai, ya zo ya ci, kuma wanda ya zo ya na son takarar ɗan majalisa, mu ka kayar da shi, duk muka tumurmursa shi. Ai ina alfahari da kaina.

To ke ba kya tunani akan cewar da ki ka yi da ke aka yi aika-aikar gama?
Wallahi mu ba aika-aika muka yi ba, zave muka yi. Maguɗi akai mana, mu ka zo, mu ka ci zaɓenmu cikin kwanciyar hankali. Saboda Allah ba ya barci. Ai mutum bai isa ya ce ya ɗauko abu ya riƙe shi, in ba Allah ne ya ba sa ba. Mu Allah ne mu ka roƙa ya ba mu, kuma mu ka shiga cikin nasara mu ka ci zaɓe. Ba wanda mu ka takura wa, mu ka ce zo ka zaɓe mu dole. Haka mutane su ka dinga bina sun ga Rashida Mai Sa’a. “wallahi mu Ganduje za mu zava, tun da ke ce akan akwati”.

Ki na so ki ce min kin taimaka gurin samun nasarar ‘Inconclusive’?
Ni ko na taimaka, taimakawa daga sama har ƙasa ba in da ban taimaka ba wallahi a dai ‘Inconclusive, kuma duk ɗan siyasa da ya karanta wannan jaridar ya san ba ƙarya na yi ba. Ba wanda bai sanni a Jihar Kano ba, kuma ba wanda bai san abin da na yi kan Ganduje ba. Kuma alhamdu lillahi, Gandujen mun ɗauke shi tamkar uba ne, shi ya sa mu ka tsaya tsayin daka don mun san ya na ƙaunarmu. Kuma mun zave shi ba mu ji kunya ba, duk wanda ya ke a Kano ya san Ganduje ya yi aiki.

To yanzu ki gayawa mutane, idan kin zama mataimakiyar gwamnan Jihar Kano, me za ki yi ma su?
Wallahi idan na zama mataimakiyar gwamna Jihar Kano zan inganta lafiya, harkar ilimi za ta yiwu sosai, a Kano za ku ga ayyuka a ƙas. Sannan kuma za a gyara tarbiyyar maza da mata. Sannan duk wani matashi zai samu aiki a ƙarƙashina. Don ni idan na zama mataimakiyar gwamna, ba zan daina amfani da foundation ɗina na Mai Sa’a Charity Foundation ba, zan ci gaba da foundation ɗin mutane a Jihar Kano. Ai mu mata a mulki an sani mu na da amana. Ba kamar maza ba ne. Mu ba ma yaudara. Wani zai zo ya na yaudarar mutane zai yi kaza, akwai wani ɗan takara muna yara da ya ce zai yi famfon fura da nono. Duk na san lokacin ina tuna ababen. Amma da ya ci gwamna, duk bai yi waɗannan abubuwan ba. Amma mu a wannan lokacin, 2023, idan Allah ya ba mu sa’a mu ka ci zaɓe, za mu dawo da Kano sabuwa fil. Za mu ɗora daga inda Baba Ganduje ya tsaya, mu kuma bijiro da wasu, in sha Allah.

To Maisa’a, Allah ya bada sa’a.
Amin ya Rabbil alamin, na gode.