Tsufa (2)

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan’uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki.

A satin da ya gabata, mona tara magana ne a kan tsufa. Na yi bayanin cewa tsufa wani mataki ne na rayuwar ɗan Adam. Yau zan ɗora daga inda na tsaya. A satin da ya wuce ɗin dai,  nayi bayanin tasirin wasu abubuwa game da saukowar tsufa, irinsu cima, muhallin da mutum ya taso a ciki, tsarin rayuwa, da sauransu.

Yau in sha Allah zan kawo irin sauye sauye da ke faruwa a jikin ɗan adam yayin bayyanar tsufa. Akwai  sauye sauye na zahiri wanda kowa zai iya gani, akwai kuma na ba]ini. Babbar alamar bayyanar tsufa ta zahiri ita ce bayyanar farin gashi da ake ce masa furfura. Furfura na faruwa ne saboda halittar da ke ba wa gashi baƙar kala ta mutu. Tunda akwai dubban silin gashi a jikin ɗan Adam, haƙiƙa akwai dubban waɗancan halittu na “enzymes” masu bawa kala gashinsa. Da ɗaya da biyu take ɓilla, a hankali a hankali m har ta mamaye ko ina, amma tafi yawa a fuska da kai. Kafin nayi gaba, ina so mu tuna cewa akwai bambanci tsakanin mutane. Wani mai saurin yin furfura ne wani ko akasin haka ne.

Abu ba biyu da ke nuna bayyanar tsufa shi ne shikawar fata. Abinda nake nufi shi ne fata za ta fara yamushewa a hankali, abinda a turance a ke Kira da “skin wrinkles”  Wannan na faruwa ne sakamakon gushewar wani jigo da ke ƙarfafa fata da ƙashi Wanda ake Kira da “collagen”.
Shi collagen wata halitta ce mai tabbatar da ƙarfi da dattakun sassan jikin mutum. Wannan halittar masana sun rarraba ta zuwa gida 7, amma a zahirin gaskiya rabe-rabensa ya kai kashi 27.

Masana jikin ]an Adam sun ce shi nau’i na farkon ƙarfinsa ya kai ƙarfe, duk da cewa girmansa bai kai aikin gashi ba. Wannan nau’i na farkon shi a ke samu a fata da ƙashi.

Akwai kuma sauye-sauye ba baɗini waɗanda iya shi wanda tsufan ya saukowa zai gani, ko zai dinga gani. Zan kawo bayanin yadda abin faruwa a ɓangarori da dama na jikin ɗan adam amma kafin nan, mutum zai fara ganin ƙarfinsa ko ƙarfinta da kuzari sun fara ha baya.  Abinda ya ke iya yi lokacin ya na ɗan shekara 20 zuwa 35 zuwa 40 yanzu ya na ɗan ba shi wahala.  Wannan shi ne babban abin da mutum zai fara fahimta na alamun saukowar tsufa. 

Yanzu kam zan kawo tasirin tsufa da abubuwan da ya ke haddasawa yayin bayyanar sa. 

  1. Raguwar ƙarfin fikira da azanci da tunani.  Wannan ya na faruwa ne saboda dalilai da dama, ciki har da raguwar kwayoyin halittar ƙwaƙwalwa.  Duk shekarar da mutum ya ƙara a rayuwarsa, to ƙwayoyin  halittar ƙwaƙwalwa suna  mutum amma ba a maye gurbinsu da wasu. Saɓanin abin da ke faruwa a wasu sassan; idan ƙwayoyin halittun wajen sun mutu a na maye gurbinsu da wasu. Amma a ƙwaƙwalwa abin ba haka yake ba. Ko shin me yasa?  Dalilin shi ne: akwai ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa da yawa, biliyoyi ne. Saboda haka idan wasu ‘yan tsirari sun mutu,  ay babu damuwa.
  2. Raguwar yawan tsokar nama a jiki. Da sannu kitse zai dinga maye gurbin da tsokar nama take a gurare daban daban. Saboda hakane ya sa ruwan jikin tsofaffi bai kai na matasa ba. Kuma a duk lokacin da suka gamu da larura mai sarayar da ruwan jiki irinsu amai ko gudawa, to su na shiga cikin mummunan haɗari kasancewar jikinsu ba ruwa da yawa, sannan kuma ga ruwan da aka rasa ta hanyar amai ko gudawa ɗin.
  3. Gaɓɓai, irinsu mahaɗar ƙashi za su fara rauni da ciwo saboda ƙarancin wani ruwa da ke cikin mahaɗar da ake Kira “synovial fluid “. Ƙarancin wannan ruwa kansa mahaɗar ƙashi ta yi tauri,  a dinga shan wahala wajen motsa ta. Abin da ke faruwa kenan a mahaɗar gwiwa, har kaga idan tsufa ya kai tsufa, tafiya ta kan gagara.  Bayan ƙarancin ruwan, abinda ke sa tsofaffi su dinga jin wahalar tafiya shi ne kaucewar ƙashin cinya daga saitin da Allah ya yi masa. Idan mutum ya na tsaya, ku ka kalli ƙashin za ku fahimci cewa ya ɗan karkato ciki, kamar dai yadda almakashin ɗinki yayi a wajen saka yatsu. Wannan shi ne yadda Allah ya saita ƙashin domin ya zauna da kyau akan ƙashin ƙafa. Domin ƙarin bayani game da wannan,  ku duba rubutun baya mai taken “Kyakkawar Siffa”.

A lokacin da shekaru su ka fara ja, wannan saitin da ƙashin ya ke da shi sai ya fara waskacewa ta yanda idan mutum ya zo tafiya,  ƙashin cinya ba zai daidaita akan ƙashin ƙauri ba, kunga kuwa dole tafiya ta yi wahala.

  1. Ƙarfin gudanar da ayyuka jiki na muhimman gaɓɓai shi ma zai fara rauni. Sai dai kuma raunin bai fiya bayyana nan take ba, ya kan ɗauki lokaci. Misali: zuciyar ɗan Adam na da ƙarfin harba jini ninki Goma na ƙarfin harba jinin da take yi a lokacin yana kwanciyar hankali.  Ma’ana za ta iya yin aiki ninki goman Wanda ya Saba yi, idan dai bu}atar hakan ta samu. To tun da zuciyar ɗan Adam ta na harba jini ya kewaya jiki sau Saba’in da biyu zuwa sau ɗari a duk minti ɗaya, ana nufin za ta harbawa sau ɗari bakwai zuwa sau dubu kenan. Sai dai hakan ba zata taɓa faruwa ba! To wannan ƙarfin aiki da ke taskance a gaɓoɓi masu muhimmanci zai Dina raguwa yayin da ɗan Adam ya ƙetare shekara 30.
  2. Hanyoyin jini ko jijiyoyin jini za su fara nauyi yayin da mutum ya ƙetare shekara 45. a mandarin mini ya dinga gudana a cikinsu a kwanciyar hankali,  sai ya yi da gaske kafin ya wuce. Me yasa? Saboda sun tsuke daga ciki. Wannan she zai sa zuciya ta dinga daddagewa ta harbo jinin da ƙarfi domin ya samu ya wuce ta hanyoyin, ya kai izuwa sassan jiki. Hakan shi yasa manya da tsofaffi mizanin gudun jininsu ya fi na matasa da yawa hawa. A dunƙule, mutum yanz ƙara shekaru ne, jininsa na ƙara hawa.
  3. Garkuwar jiki ita ma ƙarfinta zai fara baya. Cutukan da take iya yaƙa a da lokacin da mutum ya ke matashi ko matashiya sai su nemi su fi ƙarfinta.  Idan kuma su ka samu rinjaye a kanta, sai mutum ya fara rashin lafiya. Wannan shi ne dalilin da yasa tsofaffi su ka saurin kamuwa da cututtuka daga ƙananan har zuwa manyan!

Masu karatu ku tara mako mai zuwa da yardar Sarkin halitta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *