El-Rufa’i ya nemi ICPC ta biya tarar biliyan N15.6 kan kamawa da zargin ɓata masa suna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da iyalansa sun nemi Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC), shugabanta da wasu mambobin hukumar da su biya shi diyyar Naira biliyan 15.6 bisa kamawa da tsare shi da kuma zargin yin wasu kalaman ɓatanci akansa.

Hakan na ƙunshe ne a wata takardar ƙorafi dake ɗauke da 4 ga Maris 2026, wadda ta fito daga lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Ubong Akpan, kuma an kai ta hedikwatar hukumar ICPC da ke Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai na hannun ICPC tun bayan da EFCC ta bayar da belinsa a ranar 18 ga Fabrairu, 2026.

Wannan ba shi ne karo na farko da El-Rufai ke samun saɓani da ICPC ba, domin a baya ya kai ƙarar hukumar inda ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 1 kan take haƙƙinsa bayan jami’an ICPC sun kai samame gidansa.

A sabon ƙorafin da Malam Nasir El-Rufai ya kai, ya bayyana cewa yana zargin ICPC da laifuffuka da suka haɗa da ɓata suna, amfani da iko ta hanyar da bata dace ba, amfani da ƙirƙirar takardun ƙarya, gurfanarwa da mugun nufi, ƙin bin umarnin kotu, da kuma take haƙƙin ɗan-adam.

By Babaji