Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi ‘yan adawa da ruɗar da jama’a akan gyare-gyaren dokar zaɓe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki jam’iyyun adawa musamman ADC da NNPP, inda ta zarge su da yaɗa kuskure da ƙoƙarin haddasa abin da zai janyo cece-kuce acikin al’umma game da dokar zaɓe da aka yi wa kwaskwarima a kwanan nan.

A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a jiya Alhamis, fadar ta yi watsi da zarge-zargen da ‘yan adawar suka yi a wani taron manema labarai a Abuja, inda suka soki Shugaba Bola Tinubu da Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin APC.

Ya bayyana ikirarin nasu a matsayin kalaman “ƙarya masu haɗari”, yana mia cewa ‘yan adawar sun bayyana fahimtar kuskure da gangan akan hukunce-hukuncen kundin dokar da nufin ruɗar da jama’a da ƙoƙarin ƙara ɗaukaka darajar siyasarsu.

Ainihin abin da aka mayar da hankali akansa da ya haddasa rikicin shi ne gyaran dokar zaɓe ta 2026 da majalisar dokokin ƙasa ta tantance, wadda Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu a hukumance.

A cewar fadar, gyaran ya hukunta yin amfani da takardar EC8A a matsayin mafita matuƙar aka samu tsaikon miƙa sakamakon zaɓe ta na’ura.

Onanuga ya bayyana ikirarin cewa hakan zai bayar da damar yin maguɗi ba gaskiya ba ne, sai dai mafita ce da aka samar domin tabbatar da sahihancin zaɓe.

Ya ƙara da cewa, samar da shafin bayyana sakamako na yanar gizo, wato IReV da Hukumar Zaɓe INEC ta yi, abu ne da zai tabbatar gaskiya da adalci, wajen bayyana haƙiƙanin sakamakon zaɓuka.

Kazalika, ya yi tsokaci akan nuna rashin amincewa daga ɓangaren adawa akan yin zaɓukan fidda gwani kai-tsaye da zaɓe na cimma matsaya guda acikin jam’iyya a gyararriyar dokar, inda ya bayyana mamaki akan matakin nasu, yana mai cewa hakan abu ne da zai inganta dimukraɗiyyar jam’iyya da dawo da mallakarta ga asalin mambobinta daga tushe.

By Babaji