FIFA ta rage wa Afrika ta Kudu maki a wasannin neman gurbi a Kofin Duniya

Spread the love

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta ƙwace makin Afirka ta Kudu sakamakon yin amfani da ɗan wasan da aka dakatar a wani wasa.

An dakatar da ɗan wasa Teboho Mokoena ne a karawarsu da ƙasar Lesotho tun a watan Maris, 2025.

Hukuncin ya ce, an bai wa Lesotho maki uku a wasan da ci 3-0, sannnan an ci tarar tawagar ta Bafana Bafana kusan kimanin Naira miliyan 18.

Hukumar ta bayyana haka ne ta shafinta na yanar gizo a yau Litinin.

By Babaji