Gare ku mata

Spread the love

Daga ABDULLAHI YAHAYA MAIZARE

Duk fushin da za ki yi da mijinki kada ki sake ki yi masa waɗannan abubuwan:

Akwai matan da su ke wuce gona da iri a lokacin da suka samu matsala da mazansu. Dole ne a riƙa samun matsaloli a tsakanin ma’aurata, amma duk irin matsalar da za ki samu da mijinki kada ki kuskura ki masa waɗannan halayen:

  1. Duk irin matsalar da za ta faru tsakaninki da mijinki kada ki shigo da raini a tsakaninku. Ki ci gaba da masa biyayya koda ki na fushi da shi. Amma shigowa da raini ko ƙasƙanta shi saboda kun samu matsala ba naki ba ne.
  2. Duk irin saɓanin da za ki samu da mijinki kada ki daina abubuwan da kika san ki na masa waɗanda yake so.
    Idan duk safiya ke ce ke zaɓa masa kayan da zai sa, kada ki fasa masa hakan saboda ki na fushi da shi.
  3. Duk bacin rai kada ki daina dafa wa mijinki abinci. Ko da ke ce kike taimakon gidan da kuɗin abinci kada ki fasa saboda kun samu matsala.
  4. Akwai matan da idan suna fushi da maigidan sai ya shafi ‘ya’yansu. Kada ki cutar da yaranki ko na abokiyar zamanki saboda mijinki ya ɓata miki rai.
  5. Duk tsananin masifan da za ku yi da mijinki idan ya buƙace ki miƙa masa wuya. Wasu matan idan suna fushi da mazansu sai su ƙi yarda su yi kwanciyar aure da su. Wannan ba hanya bace da za ki warware matsalarku.

Da fatan mata za su kiyaye waɗannan abubuwan domin samar da ingantaccen zamantakewar aure. 

A ƙarshe ya dace mata da maza mu ƙara fahimtar tarayyar aure bautar Allah ce, ashe kenan yakamata komai za mu yi, ya zama shi Allan muke duba. Ta hakan ce kawai za mu iya haƙuri da duk wata matsala da ta tunkaro zaman aurenmu. Sannan mazan ma ku sani, duk abin da mu ka yi magana kan mace na kyautatawa, kai ma yana kanka a matsayin ka na maigida, domin littafi mai tsarki na cewa, “su na da kwatankwacin abin da ku ke da shi kansu na daga kyautatawa.”

Wannan zai tabbatar ma ba matarka ce kawai aka ɗora wa alhakin kyautata ma ka ba. Duk wani abu da za a yi gare ka don faranta ma ka rai, kai ma Musulunci ya ɗora kwatankwacin sa kanka ga matar taka. 

Da wannan na ke kira da babbar murya ga ma’aurata da su san daraja da ƙimar aure, su mutunta juna kuma su daɗaɗa wa juna don samun jin daɗi a duniya da kuma gobe ƙiyama.

By Editor