Khalifa Muhammadu Sanusi ya fitar da mutane 59 daga kurkuku a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gidauniyar Muhammadu Sanusi ll ta fitar da mutane 59 daga gidan yari, waɗanda su ka kasa biyan tara da kuma waɗanda a ka ɗaure su saboda basussuka da a ke binsu.

Da yake zantawa da manema labarai a Laraba, Shugaban gudanarwar gidauniyar, Mujtaba Abba, ya ce Khalifa ya biya kuɗaɗen tarar da na basukan mutane 59 ɗin, kimanin Naira miliyan 16,820,370.

Abba ya yi bayani cewa Khalifa ya bada umarnin a biya wa ɗaurarru 26 kuɗaɗen tara da basuka a gidan yarin Kurmawa, wanda adadin kuɗin ya kama Naira 4,466,500.

A cewar shugaban gudanarwar, Khalifa ya umarci a biya wa ɗaurarru 33 kuɗaɗen tara da basuka, wanda ya kai kimanin Naira miliyan 11,380,770.

Ya ce gidauniyar ta fuskanci cewa akwai jama’a da dama da laifukan su ba su taka kara sun karya ba, inda ya qara da cewa yawancin laifukan na rigimar bashi ne da sauran ƙananan laifuka.

Abba ya kuma yi kira ga al’umma masu halinsa su yi koyi da Khalifa Muhammadu Sanusi wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.

Ya kuma yi kira ga waɗanda su ka amfana da su zamto mutane nagari a cikin al’umma.

By Editor