Akwai buƙatar gwamnati ta sanar wa jama’a sharuɗɗan buɗe iyakar ƙasa da ta yi – Hon. Wada

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

An buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta bayyana ƙa’idojin da ya kamata al’ummar ƙasar nan su sani dangane da sake buɗe bodojin da ta bayyana ta yi cikin kwanakin nan.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin babban ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa a Ƙaramar Hukumar Nasarawa dake Jihar Kano, wato Hon. Bashir Wada, shugaban kasuwar Sabuwar Singa dake kan titin ‘Yan-kaba cikin garin Kano a wata zantawa da manema labarai.

Hon. Bashir ya cigaba da shaida wa manema labarai cewa lallai wannan yunƙuri na Gwamnatin Tarayya abu ne mai kyau da kowane ɗan kasuwa zai alfahari da jinsa, amma kuma tarnaƙin a nan shine mene ne al’umma ya kamata su rinƙa shigo da shi don kauce wa karya dokar gwamnati da kuma abinda zai iya zama koma baya a harkar kasuwanci su.

Sannan shugaban sabuwar Singar ya buƙaci mutane su fahimci cewa lallai wannan tsadar kayan da ake samu yau da gobe ba daga gare su ba ne, inda ya ce da yawan lokuta wajen sama kayan da suke shigowa da shi haraji ne ya yi yawa.

Wada ya tabbatar kashi biyar da ake ɗorawa na haraji a da ya zuwa yanzu ya koma kashi bakwai da rabi saɓanin baya, ya zama dole sai kuɗin kaya sun ƙaru saboda duk kuɗin da ɗan kasuwa ya kashe sai ya saka su cikin lissafi, shi ya sa da yawan lokuta ake ganin kamar ‘yan kasuwa ke sa wa kaya kuɗi da yawa wanda ba haka ba ne; sai an yi wa mutum bayani sannan idan mai fahimta ne ya fahimta.

Kazalika ya kuma yi la’akari da yadda ake samun tsaikon wutar lantarki a yanzu da ake ciki wannan lokaci da ita ma tana taka muhimmiyar rawa wajen sa mai ya yi tsada, wanda kuma kamfanoni ke amfani da shi da yanzu suke sayen shi kusan Naira ɗari takwas saɓanin baya a Naira ɗari shida a misali.

“Ya kamata a ce yanzu haka duk kayan da aka shigo da shi cikin gari jami’an tsaro su ƙyale su muddun an tabbatar babu wani matsala tare da wannan kayan, saboda an biya dukkan kuɗaɗen ƙa’idar shigowa da kayan,” in ji shi.

Kazalika ya kuma buƙaci mutane su kasance masu dagewa da addu’a, bayan wannan kuma akwai buƙatar gwamnati ta jajirce wajen samar da tsaro a ƙasar nan don babu tantama harkar kasuwanci ta samu koma baya ta wannan ɓangare. Za ka sayo kaya wani gari amma kana zullumin yadda za ka isa da wajen dawowa, don haka sai gwamnati da al’umma sun taimaka don magance wannan matsalolin da ake fama da su.