’Yan sanda sun yi wa Kwamandan ‘Civil Defense’ ɗanyen aiki har sun kashe dogarinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan sanda a Jihar Imo sun yi wa Kwamandan Civil Defence lilis, sa’ilin da wani rikici ya ɓarke tsakanin ‘yan sandan da jami’an NSCDC sakamakon rashin jituwan da ya wakana tsakanin jami’an hukumomin tsaron biyu. 

Manhaja ta ruwaito cewa ‘yan sandan sun kai farmaki hedikwatar NSCDC da ke Owerri, ranar Litinin, kuma suka yi wa kwamandansu zindir kana suka kashe dogarinsa. 

Rahoton ya ƙara da cewa rikicin ya fara lokacin da wani ɗan sanda sanye da kayan gida ya tare hanya, ya hana Kwamandan NSCDC wucewa yayin da yake hanyar komawa Owerri daga Abacheke, inda matatar man sata ta yi gobara. 

Wani jami’an Sibil Defence mai suna Ikechukwu ya ce: “Lokacin da dogaran kwamanda suka ce wa ɗan sandan ya tashi daga hanya, ya qi, sai ya kira sauran abokansa ‘yan sanda daga hedikwatar ‘yan sanda kuma ya bisu ofishinsu.

“Yayin da suka kai ofishin NSCDC, ɗan sandan ya sake tare hanya ya fito da bindigarsa yana iqirarin cewa shi ɗan sanda ne. Kawai sai jami’an NSCDC suka zagaye shi suka ƙwace bindigar kuma suka garƙame shi.” 

Wani jami’in hukumar wanda ya buƙaci a sakaye sunansa ya ce, “bayan an sake shi, sai ya dawo da rundunar MOPOL kuma suka shiga dukan jami’anmu suka lalata kayan ofishinmu.

“Yayin da aka fara harbe-harben bindiga, sai kwamandan ya fito sulhunta lamarin, amma ‘yan sandan suka yi masa lilis kuma suka cire masa riga suka yi awon gaba da shi,” a cewar majiyar.