Tsaro: Za a fara ɗaure masu biyan ‘yan bindiga kuɗin fansa – Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattawan Nijeriya ta zartar da wani ƙuduri da zai tabbatar da hukuncin ɗaurin aƙalla shekara goma sha biyar ga masu biyan kuɗin fansa don kuɓutar da wani da aka sace.

Ƙudurin dokar ya kuma amince da hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane.

Ƙudurin, wanda gyaran fuska ne ga dokar yaƙi da ta’addanci, ya ƙunshi ɗaurin rai-da-rai ga masu satar mutanen da kotu ta kama da laifi, kuma matuƙar satar ta kai ga mutuwar mutum, masu laifin za su fuskanci hukuncin kisa.

Ɓangaren da ke cike da ka-ce-na-ce a ƙudurin dokar dai shi ne wanda ya nemi ɗaure duk wani mutumin da ya biya kuɗin fansa ga masu satar mutane.

Hukumomi sun yi amanna cewa biyan kuɗin fansar na rura wutar sace mutane a Nijeriya, kamar yadda su ma ‘yan majalisar dattawan suka yi imani da hakan.

‘Yan majalisar Dattijan, sun ce idan aka zartar da ƙudirin, zai tsame Nijeriya daga cikin ƙasashen da ake rura wutar aikata laifuka wajen biyan kuɗi.

Wasu masu lura da al’amura a ƙasar sun ce mayar da batun laifi, zai sanya iyalan mutanen da aka sace waɗanda idonsu ya rufe kuma ba su da yadda za su yi ciki mawuyacin hali saboda ƙarancin matakai daga mahukunta na kare aukuwar sace mutane tun da farko da hanzarin ceto mutanen da aka sace idan abin ya faru.

Za a tafka muhawara kan ƙudurin dokar a majalisar wakilai kafin aikawa shugaban ƙasar don ya sa hannu, lamarin da zai iya kwashe makwanni ko watanni.

Nijeriya dai na faɗi-tashi wajen shawo kan miyagun sace-sacen mutane da gungun ‘yan fashin daji waɗanda suka sace dubban mutane a cikin shekarar da ta wuce.

Fiye da shekara 10 ke nan wasu gungun ɓatagari da ake kira da ‘yan fashin daji ke tayar da zaune-tsaye musamman wajen kai hare-hare ƙauyuka da garuruwa da kuma satar mutane don neman kuɗin fansa.

Yawanci dai su kan sace ɗalibai ko mazauna ƙauyuka da kuma waɗanda ke tafiya a kan manyan hanyoyin musamman a jihohin arewacin ƙasar.