Gidauniyar tallafawa Dimokuraɗiyya ko tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasashe?

Daga IBRAHIM YAYA

A duk lokacin da aka ambaci asusu ko gidauniya, abin da zai fadowa mutum shi ne, aikin taimako ko inganta rayuwar al’umma a fannoni daban-daban, kamar lafiya, Ilimi, muhalli, mata har ma a wasu lokuta da kananan yara da sauransu.

Sai dai sabanin irin asusu ko gidauniyar da al’umma suka sani, har ma suka ci moriyarsu, gidauniyar NED ta Amurka, wata gidauniya ce da Amurkar ta ƙirƙiro da nufin tayar da hargitsi da neman tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran ƙasashe da sunan raya demokiraɗiyya.

A kwanakin nan ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fitar da wasu jerin shaidu game da asusun demokuraɗiyya na ƙasar Amurka NED. Wadannan shaidu masu ƙunshe da manyan sassa shida da kalmomi kimanin 12,000, sun bankaɗo haƙiƙanin tsarin asusun, ta hanyar misalai guda 100 da aka tattara daga rahotanni.

Bayanai na nuna cewa, ƙasar Amurka ta dade tana amfani da karfin tuwo wajen baiwa demokuraɗiyya makamai, da yaƙi da demokraɗiyya da sunan shimfida demokuraɗiyya, da haddasa rarrabuwar kawuna, da yin katsalandan a harkokin cikin gidan wasu ƙasashe, lamarin da ya haifar da mummunar illa.

A matsayinsa na mai nuna fin ƙarfi da aikata ashsha da sunan bayar da taimako na gwamnatin Amurka, asusun NED ya keta halascin gwamnatocin wasu ƙasashe tare da bunkasa maƙiya masu goyon bayan Amurka ta hanyar fakewa da sunan “inganta tsarin demokuraɗiyya”.

Asusun NED ya kuma faɗaɗa aikin makircinsa zuwa ƙasar Sin, tare da zuba kuɗaɗen masu tarin yawa a duk shekara, don tunzura neman “‘yancin kai a Xinjiang, da Hong Kong da Tibet” don aiwatar da ayyukan kin jinin Sinawa. Haka kuma asusun ya hada kai da masu neman ‘yancin Taiwan a wani yunƙuri na haifar da rarrabuwar kawuna da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar mashigin tekun Taiwan, lamarin da ya haifar da fushi da adawa daga al’ummomi dake ɓangarori biyu na mashigin tekun Taiwan.

Ko ma dai mene ne, yanzu dai asirin wannan asusu ya tonu, kuma duk wani makirci da neman tayar da zaune tsaye ko raba kan al’ummun ƙasashe ta hanyar fakewa da gidauniya ko asusun raya tsarin demokuraɗiyya da ‘yanci ba zai taba yin nasara ba.