Adabin zamanin da na Sin

Daga AMINA XU

Taƙaitaccen bayani
Adabi, wani kashi ne mai kuzari sosai a cikin al’adun ƙasar Sin. A cikin dogon tarihi, adabin gargajiyar ƙasar Sin ya hada da manyan ra’ayoyin al’adun ƙasar Sin, ya bayyana burin jama’ar ƙasar na neman gaskiya, da alamun ƙasar na musamman. Akwai nau’o’i daban daban na adabin ƙasar Sin, kamar tatsuniyoyi na zamanin da da can, da waƙoƙin daular Tang da ta Song, da labaran daular Ming da na Qing da dai sauransu. A cikin shekaru sama da dubu ɗaya da suka gabata, an samu shahararrun marubuta da bayanai masu dimbin yawa.

A cikin bayanin da ya gabata mun yi muku bayani kan “Tatsuniyoyi na zamanin da” da “Littafi Mai Suna Shijing” da “Waƙoƙin Yankin Chu”. A wannan karo bari mu yi bayani kan “Waƙoƙin Yuefu Na Daular Han” da “Waƙoƙin Jama’ar Daulolin Arewa Da Na Kudu”.

Waƙoƙin Yuefu na daular Han
A zamanin da, Yuefu na nufin wata hukumar kula da waƙoƙi ta daular Han. Aikinta shi ne tara waƙoƙi daga jama’ar ƙasar, tare da tsara kiɗe-kiɗe dake dacewa da su. Daga bisani, waƙoƙin da hukumar Yuefu ta tara da kuma tsara su ma an kira su Yuefu. Abubuwa mafi kyau dake cikin Yuefu ta daular Han su ne waƙoƙin jama’ar ƙasar.

Wannan waka mai suna Jiangnan ta kasance wakiliyar waƙoƙin Yuefu na daular Han. Ana iya daukar ’ya’yan furannin Lotus a tabki, tare da samun ganyaye da yawa a ciki. Kifaye suna wasa a wuraren dake tsakanin ganyayen furannin Lotus.

Wannan waƙa ta bayyana ayyukan ɗaukar ’ya’yan furannin Lotus da iyalan Jiangnan suka yi mai farin ciki. Ma’anarta ita ce, lokaci ya yi na ɗaukar ’ya’yan furannin Lotus dake cikin babban tabkin Jiangnan, inda cike yake da ganyayen furanni. Kananan kifaye suna wasa a wuraren dake tsakanin ganyayen. Duk waƙar na da dadin ji sosai, cike take da alamar rayuwa.

Mafi yawan waƙoƙin Yuefu sun bayyana labarai, dukkansu kuma sun bayyana ra’ayoyin jama’a na yin murmushi ko yin fushi ko nuna damuwa ko kuma yin farin ciki. Wasu sun bayyana rayuwar mutane masu fama da talauci, wasu sun bayyana babbar illa da yaƙe-yaƙe suka kawo wa jama’a, wasu sun bayyana ra’ayin yaƙi da aure irin na tsarin mulkin sarakuna tare da gabatar da kyakkyawan buri na neman samun soyayya, wasu kuma sun bayyana taɓarɓarewar rayuwar masu kuɗi da ta zaman al’umma a zamanin da.

Waƙa mai suna “Tsuntsun Peacock ya tashi zuwa kudu maso gabas” ta fi shahara a cikin waƙoƙin Yuefu, kana doguwar waƙa ce ta farko a tarihin ƙasar Sin, inda aka bayyana wani labari mai baƙin ciki dangane da wani iyali a zamanin da.

“Tsuntsun Peacock ya tashi zuwa kudu maso gabas”, ya waiwayo bayan da ya tafi kilomita 2.5. Wata yarinya tana iya liƙe aka a yayin shekarunta suka kai 13 a duniya, tana iya samar da tufafi a yayin da shekarunta suka kai 14 da haihuwa, tana iya amfani da kayan goge mai suna Konghou a yayin shekarunta suka kai 15 a duniya, kuma tana iya karanta littattafai a yayin da shekarunta na haihuwa suka kai 16.

Liu Lanzhi, kyakkyawar mace mai hikima sosai, ta yi aure da masoyinta Jiao Zhongqing. Daga bisani, sun nuna girmamawa sosai ga juna. Amma mahaifiyar Jiao Zhongqing, ba ta so Liu Lanzhi ko kaɗan ba. A sakamakon haka, ta tilasta Jiao Zhongqing da ya kisa aurensu. Abin kaito ne! Bayan haka, su biyu sun kashe kansu tare domin tunawa da soyayyarsu, sun zama tsuntsaye mandarin duck har abada. Sun ta da kai sun yi kuka tare, har lokacin da daddare. Daga bisani, tsuntsayen Mandarin duck sun kasance alamar soyayya. Wannan doguwar waƙa ta bayyana buri da niyya matasa ta yin aure cikin ’yanci.

Waƙoƙin Yuefu na da alamar rayuwa sosai. Ra’ayoyisu da babban sakamakon da suka samu a fannin fasaha duka sun yi tasiri sosai ga bunƙasuwar waƙoƙi masu zuwa kai tsaye.

Waƙoƙin jama’ar daulolin Arewa da na Kudu
A cikin shekaru 169 da suka gabata daga daular Song bayan daular Dongjin, zuwa daular Sui, wato lokacin sake dinkuwar ƙasar Sin baki ɗaya, wannan ne wa’adin daulolin Arewa da na Kudu, da suka ƙunshi kananan daukoli 9 waɗanda su kan yi gwagwarmaya da juna.

An samu waƙoƙin jama’ar daulolin Arewa da na Kudu bayan waƙoƙin Yuefu. Mafi yawan waƙoƙin jama’ar daulolin Arewa da na Kudu, waƙoƙin soyayya ne, waɗanda suka bayyana haƙiƙanin rayuwar soyayya tsakanin mutane daban daban. Kuma mafi yawansu ne mata su kan rera, shi ya sa suna da daɗin ji ƙwarai da gaske. Waƙar Xizhouqu ta fi shahara a cikin waƙoƙin jama’ar daulolin Arewa da na Kudu.

A yanayin kaka, an ɗauki ’ya’yan furannin Lotus a wani ƙaramin tabki dake kudu. Furannin Lotus suna tsayi sosai. An kada kai domin ɗaukar ’ya’yan, waɗanda suke da tsabta sosai daidai kamar ruwa. Akwai ruwan teku da yawa, ina damuwa sabo da kana damuwa. Iskar dake kaɗawa zuwa kudu ta fahimci abubuwan dake zuciyata, har ta dauki burina zuwa wurin Xizhou.

Ma’anarta ita ce, masoyinta yana waje, bai dawo ba. Masoyiya ta je ɗaukar ’ya’yan furannin Lotus domin samun nishaɗi. Ko da yake wani tabki ne ya raba su, amma duk yankuna biyu cike suke da damuwa. A ƙarshe, masoyiya ta roki iska da ta ɗauki burinta zuwa wurin Xizhou.

Mafi yawan waƙoƙin daular Kudu na da jimloli 5, a kowace jimla kuma, akwai kalmomi 4. An fi son amfani da jimla daya domin bayyana ma’anoni biyu①. Kuma suna da alaka sosai da kyakkyawan yanayi da tattalin arziki mai albarka a Jiangnan. Ya zuwa yanzu, an samu waƙoƙin daulolin Kudu kimanin 500.

Mafi yawan waƙoƙin daulolin Arewa ’yan ƙananan ƙabilun ne suka rubuta, waɗanda suka bayyana fannoni daban daban na zamantakewar al’umma na ƙananan kabilu dake arewacin ƙasar. Sabo da a kan yi yaƙe-yaƙe a daulolin Arewa, shi ya sa akwai waƙoƙi da yawa da suka bayyana yaƙe-yaƙe. Doguwar wakar bayyana labari mai suna “Waƙar Mulan” ta fi shahara a cikin waƙoƙin daular Arewa.

A cikin “waƙar Mulan”, an samar da wata mace mai suna Mulan, wadda ta yi ado zuwa wani namiji ta shiga rundunar soja a maimakon mahaifinta. Tana da jaruntaka sosai tare da hikima. Wannan yana da ma’ana sosai a zamanin da, inda a kan dora muhimmanci sosai kan maza a maimakon mata. A sabili da haka, wannan waka ta sami karɓuwar jama’a kwarai da gaske, har ma an dauke ta zuwa film har zuwa yanzu.

Ban da waƙoƙi dangane da yaƙe-yaƙe, akwai waƙoƙin daulolin Arewa da yawa da suka rubuta ni’imtattun wurare da rayuwar makiyaya da gudun hijira, a ƙoƙarin bayyana alamar mutanen dake rayuwa a arewa mai ƙarfin zuciya, wadda take da bambanci sosai bisa alamar mutanen dake rayuwa a kudu. Bayan haka, waƙoƙin Chile, da wakokin Zheyangliu, su ma suna da shahara sosai.

Waƙoƙin jama’ar dauloin Arewa da na Kudu sun yi babban tasiri ga marubuta na daular Tang.

Bayani
Yayin da ake samar da wata jimla bisa kalmomi, a kan samu wata ma’ana da farko, tare da boye ma’ana ta daban a ciki. A kan yi amfani da kalmomi masu sauti iri daya a cikin harshen Sinanci. Misali, Lian, na nufin furannin Lotus, da jin tausayi. Si, na nufin igiya mai siriri, da bege. Li, na nufin ’ya’ya kirar Pear, da yin ban kwana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *