2023: APC ta yaba wa Adamu kan yadda ya warware rikicin jam’iyyar a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta yaba wa shugabannin jam’iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu kan yadda suka warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar.

A wata sanarwa a ranar Talata a Gusau ta hannun Yusuf Idris, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar, jam’iyyar ta yaba wa duk waɗanda suka halarci yarjejeniyar zaman lafiya.

Idris ya ce, an warware rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Bello Matawalle da tsohon Gwamna Abdulaziz Yari a hedikwatar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Ya ƙara da cewa, yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Matawalle da tsohon gwamna Yari wanda ya kawo ƙarshen rikicin cigaba ne ga jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar APC na jiha, Alhaji Tukur Danfulani ya godewa duk masu ruwa da tsaki da suka halarci yarjejeniyar zaman lafiyar.

Danfulani ya buƙaci dukkan masu goyon bayan jam’iyyar da magoya baya da masu ruwa da tsaki su gani tare da ɗaukar duk mambobi a matsayin ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *