Kamfanin Huawei ya bai wa matasan da suka kammala karatun jami’a a Habasha damarmaki a fannin fasahohin zamani na ICT

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Sashen kamfanin Huawei na ƙasar Sin dake ƙasar Habasha ya shirya taron dandali da nufin bai wa sabbin daliban da suka kammala karatun jami’a damammakin samun horo a fannin fasahar sadarwa ta zamani.

Tamire Dawud, manajan sashen bunkasa fasahar ICT a kamfanin fasahar sadarwa na Huawei dake Habasha, ya ce kafa dandali, wani ɓangare ne na burin kamfanin Huawei na ci gaba da bada horo, da samar da ilmi, ga sabbin matasan da suka kammala karatun jami’a domin horar da su game da sabbin dabarun zamani na kamfanin, da suka hada da fannonin yada bayanai, da fasahar kwaikwayon tunanin dan adam wato AI, da fasahar manyan bayanai, da makamantansu.

Dawud ya ce, dandalin ya samar da muhimmiyar dama ga ɗaliban, waɗanda gabanin hakan suke fama da wahalhalu na rashin samun horo a matakai na ƙasa da ƙasa, da damammakin neman guraben ayyukan yi.

Huawei, wanda ke aiki tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilmin ƙasar Habasha, ya bude sassan nazarin fasahar zamani ta ICTs a manyan makarantun ilmi 42 a kasar Habasha.

Fassarawa: Ahmad

By Editor