Sin ta bada gudunmawar rigakafin Sinovac da kayayyakin lafiya ga Benin

Daga CMG HAUSA

A jiya Talata jamhuriyar Benin ta karɓi rukunin alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinovac, da kayayyakin kiwon lafiya waɗanda gwamnatin kasar Sin ta bayar a matsayin gudunmawa.

Babban jami’in ofishin jakadancin Sin dake ƙasar Benin, Yan Yan, ya jagoranci bikin mika tallafin da yammacin ranar Talata, tare da babban darakta a ma’aikatar lafiyar jamhuriyar Benin, Petas Akogbeto, wanda aka gudanar a Cotonou, birnin tashar ruwan jamhuriyar Benin.

Gudunmawar dai ta kunshi kwalaben alluran riga-kafi na kamfanin Sinovac, da sirinji, da na’urar ɗaukar hoton jiki, da manyan na’urorin binciken yanayin lafiyar jiki, da famfunan sirinji masu aiki da lantarki, da gadajen kwantar da majinyata, da sauran na’urorin ayyukan kiwon lafiya iri daban-daban.

Da yake jawabi a lokacin bikin miƙa kayayyakin, Yan ya ce, tallafin da ƙasar Sin ke bai wa Benin a fannin kiwon lafiya, alamu ne dake bayyana zurfin dangantakar dake tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu da kuma kyakkyawar abota a tsakanin al’ummun ƙasashen biyu.

Ya ce, “Sin da Benin abokai ne kuma ’yan uwan juna, waɗanda ke da kyakkyawar hulɗa a fannin kiwon lafiya don yaƙi da annobar COVID-19.”

Mai Fassarawa: Ahmad