Kotu ta yi fatali da hukuncin soke Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jingine hukuncin da Babbar Kotun Umuahia a Jihar Abia, ta yanke na soke tanade-tanaden Sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022.

A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce, Babbar Kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar a gabanta, saboda a cewarta tun farko, wanda ya shigar da ƙarar, Nduka Edede ba shi da cancantar yin hakan

Kwamitin Alƙalai mai mambobi guda uku ƙarƙashin Alƙali Hamma Akawu Barka ne ya soke wannan hukuncin.

Alƙalan sun ce Edede ya gaza bai wa kotu ƙwaƙƙwarar hujjar da ya sa ya shigar da ƙara da kuma yadda Sashen Dokar Zaɓen ya shafe shi kai-tsaye.

Don haka alƙalana suka ga babu abin da ya fi dacewa face su kori ƙarar da Edede ɗin ya shigar a Babbar Kotun Umuahia mai lamba FHC/UM/CS/26/2022.

Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe na 2022, doka ce da Malisar Dattawa ta yi wa kwaskwarima wadda ta bai wa deleget da zaɓaɓɓun wkailai damar yin zaɓe a matakin jam’iyyun siyasa.