Gombe: Tsofaffin ɗaliban firamaren Bolari sun tallafa wa makarantar

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Kungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar Firamare ta Bolari, rukuni na shekarar 1991, ta sake jaddada ƙudurin ta na ƙarfafa zumunci, jinƙai da tallafa wa tsohuwar makarantar da ta yi karatu a cikinta, a yayin Babban Taron Shekara (AGM) na biyar da ta gudanar a ƙarshen shekarar 2025.

An gudanar da taron ne a harabar makarantar, inda mambobi suka yi bitar ayyuka da nasarorin da ƙungiyar ta cimma a baya, tare da tsara sabbin manufofi da dabarun ci gaba na gaba.

Da yake jawabi a taron, Ibrahim Saleh ya jaddada muhimmancin halartar tarurruka akai-akai, yana mai cewa hakan na ƙara dankon zumunci, fahimtar juna da kuma ƙarfafa ci gaban ƙungiya baki ɗaya.

Shugaban riƙo na ƙungiyar, Rayyanu Ali, ya bayyana haɗin kai da goyon bayan juna a matsayin ginshiƙan nasarar kowace ƙungiya, inda ya yi kira ga mambobi da su ƙara azama wajen haɗa kai domin cimma muradun da aka sa a gaba.

Haka zalika, Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Usman Saleh Sadauki, ya buƙaci mambobi da su nuna sadaukarwa da jajircewa, yana mai cewa babu ci gaba mai ɗorewa face an sadaukar da lokaci, ƙoƙari da dukiya.

A yayin tattaunawa, Auwal Abdullahi da Mustapha Ibrahim sun yi kira da a inganta hanyoyin sadarwa da gayyatar mambobi, tare da ƙarfafa kowa da ya nemo sauran tsoffin abokan karatu da ba su shiga ƙungiyar ba, kafin babban taro na gaba.

Wani mamba da ya halarci taron karon farko, Mohammed Jijji, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka shirya taron, yana mai cewa ya samu damar sake haɗuwa da tsoffin abokan karatunsa a cikin yanayi na farin ciki.

Haka kuma, mambobin sun yaba wa Dokta Hamza Ahmed da Usman Saleh bisa rawar da suka taka wajen taimaka wa ‘ya’yan wasu mambobi samun guraben karatu a Jami’ar Jihar Gombe, suna mai bayyana hakan a matsayin kyakkyawan misali na taimakon juna da haɗin kai.

Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a taron shi ne bai wa makarantar kayan sauti na zamani (wireless public address system), domin taimakawa wajen inganta tarukan makaranta da harkokin koyarwa da koyo.

Da yake karɓar kyautar, Shugaban makarantar, Usman Shehu, ya nuna godiya ga ƙungiyar, yana mai cewa kayan sautin za su taimaka matuƙa wajen gudanar da tarukan makaranta cikin sauƙi da tsari.

Ya bayyana cewa makarantar na da ɗalibai 4,630 da malamai 106, tare da nuna cewa makarantar ta zama mafi kyau a jihar a shekarun 2023 da 2024, abin da ya kai ga ɗaga ta zuwa matsayin Makaranta ta Musamman (Special School).

Shugaban makarantar ya ƙara da cewa a shekarar 2025, wani ɗalibi daga makarantar ya wakilci Jihar Gombe a Gasar Makarantun Firamare ta Arewa maso Gabas, inda ya samu nasara, yana mai yaba wa rukuni na 1991 bisa hangen nesa da ci gaba da tallafa wa makarantar.

Taron ya kuma yanke shawarar fifita jin daɗin mambobi ta hanyar bayar da tallafin kuɗi, shawarwari da sauran nau’o’in taimako ga duk wani mamba da ke cikin buƙata, domin ƙarfafa zumunci da jinƙai a tsakanin ‘yan ƙungiyar.

By ukarofi