Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
Alhaji Lawan Ali Gujingu daga ƙaramar Hukumar Taura Jihar Jigawa jigo ne a jam’iyar APC kuma babban tsohon ma’aikaci gwamnatin jihar Kano da Jigawa da matakin gwamnatin tarayya wanda ya yi ritaya a lokacin da ya gabata, ya bayyana cewa kasancewar gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ɗanmoɗi mutum ne haziƙi kuma wanda ya fito daga gidan malanta wanda suke ce masa ɗan liman ko Malam Imam a lokacin da suna makaranta tare mutum ne wanda ya san darajar ilimi wanda ya ba shi muhimmaci sosai musamman yadda za ka ga ilimi na daga cikin ƙudurorinsa 12 da ya yi alƙawarin raya jihar Jigawa da wannan ƙudurori 12 kuma kasancewar ɗanmoɗi tsohon malamin makaranta ne kuma tsoho ma’akacin gwamnati kuma masanin ƙididdiga kuma mai ƙwazo, hakan ce ta sa da ya zo kan mulki jihar Jigawa domin a tabbatar da an samu ilimi mai inganci sai ya ɗauko masana akan harkar ilimi da kishinsa ya ba su muƙami inda ya bai wa Alhaji Lawan ɗanzomo kuma ya bai wa Dakta Chamo muƙamin ilimi mai zurfi haka SUBEB da sauran hukumomi haka gwamna ɗanmoɗi ya yi wajen naɗe naɗen sa domin bunƙasa ilimi da ma fannonin cigaban al’ummar jihar Jigawa kamar dai yadda Alhaji Lawan Ali Gujingu ya bayyana a wata hira da manema labarai da ya yi a birnin Kano a tsakiyar makon da ya gabata.
Haka kuma ya ƙara da cewa yadda tsarin makarantu firamare da sakandare da jamioin jihar ke tafiya kasan abun ne da aka tsara domin kishin da cigaba na gwamna ɗanmoɗi domin zakaga akwai kuɗin tallafi da ake baiwa ɗalibai wanda hakan zai taimaka ma ɗalibai su yi karatu cikin walwala da ƙarancin matsaloli ga ɗalibai da ke karatu a manyan makarantu a jihar, wannan abun yabawa ne ga gwamna ɗanmoɗi ta fuskar ilimi da sauran fannoni wanda wannan ce ta sa zance ilimi ya samu buƙasa da kashi 95 cikin 100 duk da cewa sauran kudurorin 11 suma ana tafi da su domin cigaban jihar Jigawa.
Haka zalika ya ce akwai harkar inganta lafiya ta hanyar gyara asibitoci da bada magunguna kyauta ga mara lafiya da gwamnan yake aiwatarwa a wannan jihar, haka ɓangaren kyautatawa maaikata zakaga an dawo da tsarin shagunan tsimi da tanadi ta yadda ma’aikaci zai je ya siya kayan buƙatun yau da kullum ta hanyar amfani da wani kati na zamani ta yadda mutum ɗaya banzai sayi kaya ya siyar ba an tsara dole in mutum zai saya ba zai wuce sau ɗaya ba a wata ba ga kuma tallafi iri-iri na koyar da sana’o’i da tallafawa al’ummar Jigawa da kayan masurufi a lokuta daban-daban domin rage musu raɗaɗi. Ga kuma harkar bunƙasa noma da kiwo a jihar da dai sauransu.
A ƙarshe Alhaji Lawan Ali Gujingu ya bayyana cewa a matsayinsa na ɗan APC ya san shugaban ƙaramar hukumar Taura da sauran ƙananan hukumomi da aka zaɓa suna ƙokarin su dai dai gwargwado wanda abin a yaba musu ne haka in kazo wannan ƙaramar hukumar za ka ga cewa shugaban ƙaramar hukumar tamu na ƙokarin faɗaɗa kasuwar Gujingu domin rage cunkoso a wannan kasuwa ta Gujingu da sauran kasuwanni a wannan ƙaramar hukuma haka kamar a matakin jiha.
Shi ma shugaban ƙaramar hukumar ba a bar shi a baya ba wajen haɗa kai da jami’an tsaro da sarakuna da manoma da sauran al’umma domin kawo cigaba a ƙaramar hukumar kamar yadda yake a matakin jihar Jigawa kamar yadda Alhaji Lawan Ali Gujingu tsohon ma’aikaci wanda ya yi ritaya a matsayin darakta a matakin aikin gwamnati kuma ya yi karatun digiri har uku a gida da wajen Nijeriya da zuwa aikace-aikace da ziyarori a ƙasashen Turai da Afirka a matsayinsa na ma’aikacin gwamnatin tarayya da ya yi ritaya wanda yanzu haka ya nemo aikin ya kawo aikin yin rijiyar burtsatse mai aikin da hasken rana 1500 da ƙungiyoyi jinƙai na duniya za su bai wa Jigawa kyauta da sahalewar Gwamna Danmoɗi.
