Gwamna Lawal Dare ya yi jimamin rasuwar almajirai 17 a gobarar da ta auku a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare ya aika saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan almajirai 17 da suka rasa rayukansu a yayin gobarar da ta afka musu a wata makarantar allo a jihar.

A wata sanarwa daga Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, Lawal Dare ya bayyana hakan a matsayin abin alhini da kuma tausaya wa ga waɗanda iftila’in gobarar ta shafa.

A ranar Talata ne lamarin ya faru a makarantar allo ta Mallam Ghali dake ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda.

Ya ce, a madadin Gwamnatin jihar, suna miƙa ta’aziyarsu ga iyalan mamatan da makarantar da kuma ƙasa baki ɗaya bisa rasuwar yaran.

Ya kuma yi addu’ar fatan samun waraka cikin ƙanƙanin lokaci ga waɗanda suka samu raunuka da kuma juriyan rashin waɗanda aka rasa ga iyalansu.

Har’ilayau, Gwamna Lawal ya ce a matsayin gwamnatinsu na wacce take ƙoƙarin sauke nauye-nauyen da ke kanta, za su yi bincike game da musabbabin faruwar al’amarin gami da ɗaukar matakan kariya akan sake aukuwar irin haka a nan gaba.

Kazalika, ya ce za su tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafe ta hanyoyin da suka dace.

By Babaji