Gwamna Raɗɗa zai tafi hutun makonni uku domin duba lafiyarsa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan zai fara hutun ne daga 18 ga Agusta, 2025.
Wannan bayani ya fito ne daga kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango a wata takardar sanar wa da ya fitar.

Malam Dikko Raɗɗa ya nuna godiyarsa bisa goyon baya, fahimta da addu’o’i da al’ummar jihar ke yi masa bayan samun hatsarin da yayi.

Ya jaddada ƙudurinsa na komawa bakin aiki da sabuwar kuzari da jajircewa bayan kammala wannan hutu na duban lafiyar shi.

“Ina miƙa godiya ta ga kowa bisa kalaman alheri da goyon bayan da kuke nuna min,”inji Raɗɗa.

Wannan matakai na kula da lafiya yana da muhimmanci domin in ci gaba da gudanar da ayyuka yadda ya kamata domin ci gaban jihar mu,”ya ce.

Ya bayyana fatan sa na dawowa bakin aiki nan da zarar an kammala binciken lafiyar sa.

Gwamna Raɗɗa ya kuma ya sanar da miƙa ragamar shugabancin jihar ga Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal, domin riƙe ragamar mulki a matsayin muƙaddashi yayin wannan hutu.

Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa mataimakin gwamna zai ci gaba da tafiyar da al’amuran gwamnati da irin wannan jajircewa da kishin ƙasa.

“Muna tabbatar wa jama’a cewa dukkan shirye-shirye, tsare-tsare da ayyukan ci gaba za su ci gaba da tafiya yadda aka tsara ba tare da tsaya wa ba,”inji Dikko.

By ukarofi