Gwamnan Kano ya aike wa Majalisar Dokoki sunayen mutum shida domin tantancewa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya turawa Majalisar Dokokin jihar sunayen mutum shida domin ta sahale masa ya naɗa su a matsayin sabbin Kwamishinoni a gwamnatin sa.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Rt. Honarabul Jibril Isma’ila Falgore ne ya karanta takardar da gwamnan ya aiko a zaman majalisar na safiyar yau Litinin.

Sunayen da Gwamnan ya tura sun haɗar da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin da akawun jihar Kano da sauran su kamar haka

  1. Shehu Wada Sagagi
  2. Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya
  3. Dakta Isma’il Ɗan Maraya
  4. Ɗahiru Muhammad Hashim
  5. Injiniya Gaddafi Sani Shehu
  6. Kwamared Abdulkadir Abdussalam.

Matakin Gwamnan dai na zuwa ne bayan da ya yi wa majalisar zartarwar sa garambawul a makon da ya gabata yayin da ya cire wasu Kwamishinoni bayan ya canza ma wasu ma’aikatu.

By ukarofi