Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya bayyana ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu, Sanata Garba Musa Maidoki, a matsayin maƙaryaci kuma masharranci, wanda ke baza ƙarerayi domin cimma burin ransa.
Kwamred Idris yana magana ne a Birnin Kebbi ranar Talata, a lokacin da yake karɓar ɗaukacin masu yima Sanata Maidoki yaƙin neman zaɓe da suka ƙunshi jagororin kampen, watau, campaign coordinators, waɗanda a yanzu suka yi ma Gwamna Nasir Idris da gwamnatinsa, mubaya’a.
Gwamna Idris yaji takaicin cewar Maidoki ya kada girmansa, ya yi maganganu da basu dace da matsayinsa ba na ɗan Majalisar Dattijan Tarayyar Najeriya.
Kwamred Idris yace Maidoki yayi zargin cewar gwamnan ya hana shi tsayawa takarane na komawa Majalisa, saboda yana maganganu akan harkokin tsaro.
Gwamna Idris yace, wannan magana ƙarya ce, saboda Maidoki ko takardar tsayawa takara na APC bai saya ba.
Yayi nuni da cewar Maidoki yaji tsoron karawa da ɗan takarar da aka tsayar ne, a wurin zaɓen fidda-gwani, (primary election), saboda irin martabar da ɗan takarar yake da ita.
Yace mutanen Kebbi ta Kudu, shaida suke cewar Maidoki bai taɓa halartar wani taron da gwamnati ke shiryawaba akan harkokin tsaro da nufin magance lamarin, a inda duk masu ruwa da tsaki na halarta, amma ban da shi.
Gwamnan ya ce babu wata gwamnati da aka taɓa yi a Jihar Kebbi da ta ba lamarin tsaro muhimmanci kamr tasa, a inda yake samarwa hukumomin tsaro motocin sintiri masu yawa, da kayayyakin aiki da kuma kulawa da rayuwarsu, kuma yana ci gaba da ɗaukar wannan nauyin.
Ya ce abin takaicine cewar babu wani abu da Maidoki ya bada gudunmawa wurin harkokin tsaro, ko da kuwa keken hawa ne.
Gwamnan ya ƙalubalanci Maidoki da ya nuna wani aikin raya al’umma guda ɗaya tak da ya aiwatar ma jama’ar da ke yankin mazaɓarsa ta Kebbi ta Kudu, duk da cewar a kowani wata, ana bashi miliyoyin Naira da ya ƙunshi na gudanarda ayyukan mazaɓa, (Constituency Projects).
Kwamred Idris ya jaddada ƙudurinsa na wanzar da yima al’ummar Masarautar Zuru da sauran yankuna, ayyukan inganta rayuwarsu.
Ya buƙaci jama’a su ci gaba da bashi goyon baya domin ƙara ƙaimi wurin ayyukan bunƙasa tattalin arzikin al’ummomin jihar da ya riga ya fara aiwatarwa a duk lungu-lungu da saƙo-saƙo na Kebbi.
Gwamnan ya nuna godiya dangane da goyon baya da soyayyar da jama’ar Zuru suke bashi, yana mai bada tabbacin cewar, zai wanzar da baiwa kowa-da-kowa ƙwarin gwiwa da cikakken taimako na sauƙaƙa harkokin yau-da-kullum, da inganta rayuwar al’umma, akan turba ta samar da romon dimokuraɗiyya.
Ya yi tambihi gare su da su guje ma ‘yan siyasa da wasu shugabanni waɗanda ba abinda suke haifar ma al’umma face lalura da wahala, yana mai cewar irin waɗannan mutanen, ba abin bi bane.
Kwamred Idris yace gwamnatinsa a tsaye take wurin biyama jama’a muradunsu da buƙatunsu na rayuwa.
A jawabai daban-daban da suka yi, Shugaban Kodinetoci, (Campaign Coordinators) na Jiha, na ƴakin-neman zaɓen Maidoki, Alhaji Bello Doya, da kuma Shugaban yanki, Alaramma Abubakar Atiku, sun yi bayanin cewar gaba ɗayan jama’arsu suka sauya mubaya’arsu, daga Maidoki zuwa ga Gwamnar Jihar Kebbi, Kwamred Nasir Idris, suna masu biyayya gare shi da kyakkyawar zuciya.
Sun bada tabbacin cewar za suyi ma gwamnan aiki tuƙuru wurin cimma nasara a zabuɓɓuka masu zuwa, ya sake dawowa karo na biyu, da kuma samun nasara ga sauran ‘yan takarar APC a dukan matakai na mulki.
