Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da Naira biliyan 545,014 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2025 a ranar Alhamis ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, inda a cikin kasafin ya yi cikakken tanadin biyan ma’aikatan jihar sabon tsarin albashi na Naira 70,000.
A cewarsa, kasafin kuɗin na tafiyar da ayyukan yau da kullum ya tsaya akan Naira biliyan 151,680, wanda shine kashi 28% na jimillar kuɗin da ake kashewa, inda ya ce, da gaske za a biya kuɗin ma’aikata, da suka haɗa da ƙarin mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, fansho, gratuti da kuma samar da sababbin ma’aikata, yayin da jimillar Naira 393,334,575,000 ya tanada, don ƙaddamar da manyan ayyuka.
Gwamna Dauda ya kuma ƙara da cewa, a cikin jimillar ƙididdigar, an ware Naira biliyan 112,855,094,440, wanda ke wakiltar kashi 20.71% na ɓangaren gudanarwa.
A ta bakinsa, “wannan ɓangare ya shafi fannonin da suka haɗa da harkokin addini, yaɗa labarai da al’adu, tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, al’amuran majalisa, ma’aikatan gwamnati, harkokin majalisar zartarwa da kuma ayyuka na gabaɗaya.”
A cewarsa, ɓangaren tattalin arziki, wanda ya ƙunshi noma, kasuwanci, masana’antu da yawon buɗe ido, samar da ababen more rayuwa, gidaje da raya birane da karkara, kasafin kuɗi da tsare-tsare da kuɗi, za su samu Naira biliyan 253,239,622,000, wanda ke wakiltar kashi 46.46 na jimillar kasafin kuɗin.
A ɓangaren zamantakewar da ta ƙunshi ilimi, lafiya, matasa da cigaban wasanni, mata da cigaban al’umma, muhalli da albarkatun ƙasa, Gwamna Dauda ya bayyana cewa, an ware Naira 170,164,398,560, wanda ke wakiltar kashi 31.22 a kasafin kuɗin.
“Ilimi da lafiya, kasancewarsu mafi mahimmancin sassan, suna karɓar mafi girman kaso na 14.62% da 11.77%, bi da bi,”, ya ƙara da cewa, “a halin da ake ciki kuma ɓangaren shari’a an ware zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 8,755,460,000,” yana mai jaddada cewa, za a aiwatar da manyan ayyukan babban birnin jihar a shekarar 2025.
“An tsara kasafin kuɗin shekarar 2025 ne tare da yin la’akari da yanayin tattalin arziki da ake ciki, domin tabbatar da cewa, abubuwan da muka sa a gaba sun dace da muradun al’ummarmu da kuma manufofin kawo sauyi na wannan gwamnati,” inji Gwamna Lawal.
Ya kuma yi kira ga ’yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da su tallafa wa burin da aka samu a cikin wannan kasafin kuɗi na gaggauta aiwatar da kasafin kuɗin, “a matsayinmu na iyalin juna ta fuskar aiki, ya kamata mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin an cimma manufofin da aka zayyana, domin ci gaban jiharmu mai albarka,” inji shi.
A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Ismail Moriki, ya yi alƙawarin yin nazari dalla-dalla akan abin da kasafin kuɗin ya ƙunsa, domin a gaggauta zartar da shi kafin lokaci mai tsawo.
