Gwamnatin Kano ta ɗaukaka ƙara bayan kotu ta wanke Garo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Jihar Kano ta shigar da ƙara a kotun ɗaukaka ƙara da ke Kano, bayan babbar kotun jihar ta yi watsi da shari’ar da ake yi wa tsohon kwamishina, Murtala Sule Garo, da wasu mutane.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa an shigar da ɗaukaka ƙarar ne a ranar 12 ga Maris, 2026, watanni tara bayan kotun ta soke shari’ar. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun matsin lamba da neman a naɗa Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Takardun kotu sun nuna cewa gwamnatin jihar, a matsayinta na mai ƙara, na ƙalubalantar hukuncin da Mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya yanke a ranar 30 ga Yuni, 2025, a shari’a mai lamba K/133C/2024.

Karar ta haɗa da Murtala Sule Garo, ‘yan uwansa Muhammad da Mustapha Sule Garo, Isah Musa Kera da kuma wasu kamfanoni.

Gwamnatin na neman kotun ɗaukaka ƙara ta sake duba hukuncin gaba ɗaya.

A baya, kotun ta yi nazari kan ko an gudanar da sahihin bincike kafin shigar da ƙarar, da kuma tasirin wasu hukuncin kotun tarayya da suka shafi batun.

Idan za a iya tunawa dai, a watan Yuni 2024, gwamnatin Kano ta tuhumi Garo da ‘yan uwansa biyu da laifuka bakwai da suka shafi zargin karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da suka kai biliyoyin naira.

An zarge su da karkatar da sama da Naira biliyan 2.8 daga asusun daidaita kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Haka kuma, gwamnati ta yi zargin cewa an yi amfani da wasu daga cikin kuɗaɗen wajen sayen kadarori a ƙasar Saudiyya.

ƙarar ta haɗa da wasu ma’aikata da kamfanoni, inda ake zargin an karkatar da kuɗaɗe ta hanyoyin asusun kamfanoni daban-daban domin amfanin kai.

Sai dai kotun jihar Kano ta yi watsi da shari’ar, tana mai cewa ba a bi ka’idojin bincike yadda ya kamata ba kafin shigar da ita.

Yanzu dai ana sa ran kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatin jihar ta shigar.

By ukarofi