Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
A ƙoƙarin inganta muhalli da kawar da gurɓatacciyar iska, gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirin dashen bishiyoyi miliyan 5 a faɗin jihar.
A cewar, gwamnatin wannan tsari shi ne irinsa na farko a tarihin jihar kuma za a aiwatar da shi ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Kwamishinan Muhalli, Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan a ranar Talata jim kaɗan bayan gabatarwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu tsarin da Gwamnatin Kano take da shi na kawar da gurɓatacciyar iska da inganta muhalli gami da yaƙi da zaizayar ƙasa wanda gidauniyar Aminu Magashi ta shirya.
Taron wanda shi ne karo na 3 ana shirya shi don tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan fannonin da suka shafi ci gaban al’umma da kasafin kuɗi.
“Dashen bishiyoyi da muke shirin yi wannan karon in Sha Allah shi ne za mu dasa bishiyoyi miliyan 5, wasu za su iya cewa abin wasa muna tabbatarwa da mutane cewa, za mu samar da Platform wanda da al’ummar jihar Kano ne da kansu za su yi dashen bishiyoyin, kuma kamar yadda na miƙa goron gayyata ga gidauniyar Aminu Magashi domin wannan aikin.”
Kwamishinan ya ce za su tabbata duk bishiyoyin da aka dasa sun samu kula ba tare da an sare su ba.
“Alwashin da muka ɗauka shi ne duk bishiyun da aka samar za a kula da su, za mu ɗauki ƙungiyoyi da samar da Platforms don tabbatar da ana kula da su.”
Haka kuma, ya bayyana cewa Gwamnatin Kano na shirin ƙawata manyan titunan biranen Kano da bishiyu kamar yadda aka yi wa titin Lodge road.
Shi ma a nasa, jawabin Shugaban Gidauniyar Aminu Magashi dake tallafawa al’umma, Dakta Aminu Magashi Garba ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da ƙungiyoyin ci gaban al’umma ke shirya taron.
“Mun tattauna kan yadda za mu hada kai da ƙungiyoyi da gwamnati wajen yadda za a tunkari matsalolin harkar muhalli da suka shafi iska gurɓatacciya.
“Akwai doka da aka yi wajen magance waɗannan matsaloli da kuma zaizayar ƙasa inda mutane suka fito da matsalolin su kuma za a duba aga yadda za a magance wannan matsalar.”
