Gwamnatin Tarayya da haɗin gwiwar CIS sun ƙaddmar da tsarin bada hayar Adaidaita sahu mai sauƙi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta haɗa gwiwa da kamfanin Century Information Systems Ltd. (CIS) da kuma ƙungiyar Masu Baburan Adaidaita Sahu ta ƙasa (NATOMORAS) domin ƙaddamar da wani tsari na haya (leasing) mai inganci.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Kamfanoni na Hukumar Rajistar Haya ta Kayan Aiki (ELRA), Mista Adebola Sunday, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Sunday ya ce an ƙirƙiro wannan tsari ne domin kawo ƙarshen tsarin saye da biyan kuɗi a hankali (hire purchase) mai cike da danniya da ake yi wa masu tuƙin babura da adaidaita sahu a faɗin ƙasar.

Ya ambato Shugaban ELRA, Mista Donald Wokoma, yana cewa wannan haɗin gwiwa wani babban mataki ne na inganta shiga harkokin kuɗi da kuma ƙarfafa tattalin arziki ga masu aikin sufuri.

Wokoma ya bayyana cewa wannan shiri zai sauƙaƙa wa masu sana’ar samun babura da adaidaita sahu ta hanyar rage nauyin kuɗin farko da kuma tsauraran sharuɗɗan biyan kuɗi da suka daɗe suna addabar su.

A cewarsa, masu tuƙin za su amfana daga tsarin haya mai sassauƙa wanda zai sa su iya mallakar abin hawa cikin sauƙi.

“Tsarin haya yana buɗe ƙofa ga mutane da dama da a baya ba su da damar shiga harkokin tattalin arziki,” inji shi.

“Ta hanyar cire nauyin kuɗin farko da kuma samar da tsarin biyan kuɗi mai tsari, masu aiki za su iya adana kuɗi, ƙara yawan aiki da kuma samun ƙarin kuɗin shiga a kullum.”

Ya ƙara da cewa samun sabbin babura da masu kyau zai rage yawan lalacewa da kuma inganta aikin sufuri.

Shi ma Daraktan Kamfanin CIS, Dakta Abdul Balarabe, ya ce za su yi amfani da fasaha, ciki har da tsarin sa ido (tracking), domin ƙara tsaro da kuma tabbatar da ingantaccen amfani da kayan da aka bayar.

Ya ce wannan zai taimaka wajen rage sata, sauƙaƙa dawo da kayan da aka rasa, da kuma ƙara tsaron masu tukin da fasinjoji.

Balarabe ya kuma ƙara da cewa kamfanin zai ci gaba da haɗa ƙungiyoyi, da sauran masu ruwa da tsaki cikin tsarin domin faɗaɗa damar samun tallafin kuɗi da mallakar kayan aiki.

A nasa ɓangaren, Shugaban NATOMORAS na ƙasa, Alhaji Usman Gwoza, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa wannan wata dama ce da aka daɗe ana jira ga mambobinsu da ke fama da tsadar lamuni da kuma wahalar biyan kuɗi.

Ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ƙarfafa mambobinta a faɗin ƙasa su shiga cikin shirin, yana mai cewa zai taimaka wajen samar da mutunci, daidaito da ‘yancin kai na kuɗi ga masu tuƙin.

By ukarofi