
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 1 ga watan Mayu, 2026 a matsayin rana hutu domin karrama Ranar Ma’aikata ta duniya ta 2026.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da haka a madadin gwamnatin, a wata sanarwa da Babbar Sakatariyar a ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani ta fitar a ranar Laraba.
Da ya ke taya ma’aikata murnar zagayowar ranar ta bana, ministan ya yaba wa ma’aikatan Nijeriya bisa jajircewa da sadaukarwarsu wajen samar da ci-gaba a ƙasa.
Tunji Ojo ya kuma buƙaci ma’aikatan da su zama masu kishin ƙasa, ƙwazo da sadaukar da kai akan aiki, tare da bayyana cewa waɗannan ɗabi’u na da matuƙar muhimmanci ga ci-gaban ƙasa.
