
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke tsarin karatun ƙaramar sakandare (JSS) da babbar (SSS), tare da samar da tsarin karatun shekaru 12 a matakin farko kafin shiga makarantun gaba da sakandare ga ɗalibai.
Da haka ne Gwamnatin Nijeriya ta nemi kawo ƙarshen tsarin 6-3-3-4 da maye gurbinsa da 12-4.
Hakan zai taimaka wajen bin ƙa’idar cika shekaru 16 gabannin shiga manyan makarantu ga ɗaliban, wanda Majalisar Zartarwa kan Ilimi ke ƙoƙarin tabbatar da cewa ana aiwatarwa.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya bayyana haka a ranar Alhamis, a yayin zaman Majalisar na musamman na shekarar 2025.
A gudanar da babban taron ne a Abuja, wanda ya samu halartar kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da Abuja, hukumomi da ƙungiyoyi da ke ƙarƙashin Ma’aikatar da sauran masu-ruwa-da-tsaki.
Ministan ya ce maye gurbin karatun sakandare da na ‘Basic Education’ zai taimaka wa ɗaliban wajen kai shekaru 16 mafi ƙaranci kafin su kammala.
Ya kuma ce tsarin ya dace da yadda ake tafiyar da harkar ilimi a mataki na duniya.
Dakta Alausa ya bayyana hakan a matsayin tsarin da zai taimaka wajen ragen adadin ɗaliban da ba sa iya biya kuɗin karatu wanda a saboda haka ne suke ajiyewa ba tare da sun kammala ba.
Har’ilayau, ya ce tsarin zai samar da hanyoyin koyon ayyuka da sana’o’in da ɗalibai za su dogara da su wajen ɗaukar ɗawainiyarsu.
Ya ƙara da cewa, za a samu sauye-sauyen tsare-tsare, da faɗaɗa ababen more rayuwa, horar da malamai, ɗaukar aiki da dai sauransu a ƙarƙarshin tsarin, yayin da gwamnati ke cigaba da ƙoƙarin bunƙasa ɓangaren a Nijeriya.
