
Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta fara gurfanar da gungun waɗanda ake zargi da ta’addanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa a bayaa an gurfanar da tarin ‘yan ta’addan ne a Kainji da ke jihar Neja.
Mafi yawan alƙalan babbar baabbar kotun tarayyar suna hutu daga 7 zuwa 13 ga Afirilu. Za a dawo zaman kotu ne a ranar Talata 14 ga watan Afirilu a dukkan manyan kotunan.
NAN ta rawaito cewa akwai ɗakunan shari’a 13 a shelkwatar babbar kotun tarayya da ke Abuja da suke gudanar da shari’ar laifukan ta’addancin a ranar Talata da safe.
Wasu daga cikin alƙalan sun haɗa da Binta Nyako, Emeka Nwite, Musa Liman da Akpan Ekerete.
Rotimi Oyedepo, babban lauyan a Najeriya da daraktan hukumar gurfanar da masu laifi ta gwamnatin tarayya ne suka jagoranci tawagar lauyoyin gwamnati wajen gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban mai shari’a Mrs Nyako.
Aliyu Abubakar, shi ne darakta-janar na kawo wa masu laifi ɗaukin shari’a wanda ya jagoranci lauyoyi masu kare wasu mutane 20 da ake zargi da laifukan ta’addanci.
Wasu daga cikin waɗana ake zargin da aka gurfanar a gaban mai shari’a Mrs Nyako sun haɗa da: Hamat Modu, Isah Ali, Awal Bello, Shehu Bukar, Alhaji Kulle, Mohammed Abacha Hassan, Aminami Mallum, Tasiu Yakubu, Abdullahi Ali da sauransu.
Haka kuma an saka jami’an tsaro sosai a kewayen Babbar Kotun da dukkan hanyoyi da za su kawo mutu zuwa kotun a yayin da jirgin ‘yan sanda mai saukar ungulu ya riƙa kewaye yankin da kotun take.
