Gwamnatin Tarayya za ta mayar da yara 500,000 zuwa makaranta

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon shiri na rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma magance matsalar rashin iya karatu a faɗin ƙasar.

A ranar Talata a birnin Abuja, Hukumar Yaƙi Da Jahilci Ta ƙasa [National Commission for Mass Literacy, Adult and Non-Formal Education] (NMEC)ta fara horar da masu tattara bayanai na tsawon kwanaki biyu kan yadda ake amfani da kayan aikin tattara bayanai na zamani.

Muƙaddashin Sakatare Janar na NMEC, Dakta John Onimisi, wanda shi ne shugaban tawagar masu buƙatar tantancewa, ya bayyana cewa shirin zai bai wa fiye da ɗalibai 500,000 damar shiga makarantu a matakin farko.

Ya ce aikin zai mayar da hankali kan matasa daga shekaru 15 zuwa sama da suka daina makaranta ko kuma waɗanda ba su samu damar ci gaba da karatu ba.

Shirin, a cewarsa, ba zai tsaya kan karatu kaɗai ba, har ma da koyon sana’o’in dogaro da kai domin waɗanda suka kammala karatun za su iya shiga shirye-shiryen koyon sana’a.

Shirin zai shafi dukkan ƙananan Hukumomi 774 na ƙasar, inda aka horar da mutane 376 masu tattara bayanai daga jihohi 36 da birnin tarayya, sannan kuma za a tura malamai 250 domin gudanar da aikin a Abuja.

Za a gudanar da zangon farko na karatun tsakanin watanni 6 zuwa 9 gwargwadon tsawon lokutan koyarwa.

By ukarofi